An kori fusataccen fasinja bayan yunƙurin ƙone jirgin Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026 Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya cire wani fasinja daga jirginsa na P47866 da ke aiki a Abuja bayan ya yi barazanar cewa fushinsa ka iya babbake jirgin yayin ake ƙoƙarin kama hanyar tafiya.

A cewar wata wallafa ta X a ranar Litinin ta hannun Daraktan hulɗa da jama’ar Hukumar Bai wa Kwastomomin Jiragen Fararen Hula Kariya ta Ƙasa (NCAA), Michael Achimugu, Celestine Ezeudu, wanda shi ne fasinjan, an zarge shi da ƙin bin umarnin ma’aikatan jiragen na a daina ɗaukar hotuna da killace wayoyin hannu yayin da jirgin ke shirin tashi.

Achimugu ya ce, al’amarin ya yi ƙamari ne a lokacin da ya rikiɗe ya zama hayaniya, inda fasinjan ya yi barazanar “ƙone jirgin”.

A yayin haka ne aka hanzarta sanar da kyaftin ɗin jirgin, wanda ya sa jirgin ya juyo da misalin ƙarfe 3:57 na yamma, lamarin da ya haifar da cire fasinjan.

Shugaban na NCAA ya ƙara da cewa, abokin tafiyar Ezeudu shi ma ya fice daga jirgin don raɗin kansa yayin al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply