An taɓa tsare ni saboda neman shugabancin ƙaramar hukuma – Zulum

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana yadda a wani lokaci ’yan sanda suka taɓa tsare shi, saboda kawai ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar shugabancin ƙaramar Hukumar Mafa da ke jihar, inda ya bayyana cewa wannan ne karo na farko kuma na ƙarshe da ya taɓa bayyanar da kansa cewa, yana son neman wani zaɓaɓɓen muƙami.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC na Jihar Borno, a zauren taro na musamman da ke Gidan Gwamnatin jihar a Maiduguri.

Ya bayyana cewa abin da ya faru a Mafa shi ne kaɗai lokacin da ya taɓa bayyana da kansa aniyarsa ta neman wani zaɓaɓɓen muƙami a rayuwarsa. Ya tuna yadda burinsa na zama shugaban ƙaramar hukumar ya kai ga kama shi da tsare shi.

Da yake ba da labarin abin da ya faru, gwamnan ya ce yana ɗibar ruwa daga rijiya a Mafa, hannayensa sun yi ƙuraje kuma sun jiƙe da jini, a lokacin ne ya yanke shawarar bayyana aniyarsa ta neman shugabancin ƙaramar hukumar, yana fatan yin amfani da muƙamin wajen samar wa al’ummar yankin rijiyoyin burtsatse.

“Ina Mafa ina ɗibar ruwa daga rijiya, hannayena sun yi ƙuraje kuma sun jiƙe da jini. A lokacin ne na bayyana aniyata, na roƙi Allah Ya ba ni muƙamin domin in haƙa rijiyoyin burtsatse a Mafa. Amma wasu mutane suka kai rahoton cewa na shiga NADECO ko duk abin da suke kira ƙungiyar, wai ina ƙoƙarin tunzura jama’a kan jami’an ƙaramar hukumar, aka kuma tsare ni,” in ji Zulum.

Gwamnan ya lura cewa tsarewa na iya zama wani abu da ba za a iya kauce masa ba a wasu lokutan fafutukar siyasa. Ya ce saboda haka ba zai yi mamaki ba idan aka kama wani mutum a yayin gwagwarmayar siyasa.

“Saboda haka, ba zan yi mamaki ba idan ’yan sanda suka kama wani a lokacin fafutukar siyasa,” inji shi.

Da yake jawabi ga ’yan jarida, Zulum ya kuma yi tsokaci kan nauyin da ke tattare da shugabanci, inda ya jaddada cewa tafiyar da harkokin jiha na buƙatar sadaukarwa, haƙuri da jajircewa sosai.

Ya bayyana cewa yawan ayyukan da yake gudanarwa a kullum ya kai matsayin da a kai a kai yake barin ofishinsa tsakanin ƙarfe 11:30 na dare zuwa 1:30 na dare.

Gwamnan ya kuma yi amfani da taron wajen mayar da martani kan suka daban-daban da ake yi masa, ciki har da zarge-zargen da suka shafi kama masu zanga-zangar baya-bayan nan da suka yi amfani da taken “Tinubu Must Go”.

Yayin da yake musanta hannu a lamarin, Zulum ya ce sai washegari da safe ne ya samu labarin abin da ya faru a masallacin, amma dole ya ɗauki alhakin lamarin saboda al’umma ne suka zaɓe shi.

“Allah Ya sani, sai washegari da safe ne na samu labarin abin da ya faru a masallacin. Amma dole ne in ɗauki nauyin lamarin saboda su ne suka zaɓe ni,” inji shi.

Yayin da yake gab da kammala wa’adinsa na mulki, Zulum, wanda ake ganin yana cikin tsirarun gwamnoni da suka ƙi amincewa da matsin lambar neman su tsaya takarar Sanata ko wani zaɓaɓɓen muƙami bayan barin kujerar gwamna, ya yi kira da a yi afuwa, sulhu da haɗin kai.

Ya tuna wani lokaci na ibada da ya yi a Ka’aba mai alfarma da ke Makka, inda ya yi addu’a tare da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ya yi amfani da wannan damar wajen yafe wa duk wanda ya taɓa yi masa laifi, tare da neman afuwar duk wanda wataƙila shi ma ya yi wa laifi.

Gwamnan ya buƙaci ’yan takarar da suka nuna ɓacin rai sakamakon rashin samun nasara a zaɓen fitar da gwani na APC da su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, su haɗa kai domin samun nasarar jam’iyyar a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

A cewarsa, Allah ne kaɗai ke ba da mulki ga wanda Ya so, kuma duk wanda ya karɓi sakamakon fafatawar siyasa da kyakkyawar zuciya, Allah zai iya musanya masa da wani abu mafi alheri.

“Allah ne kaɗai ke ba da mulki ga wanda Ya so, kuma idan ka karɓi sakamakon da kyakkyawar zuciya, Zai musanya maka da wani abu mafi alheri,” inji Zulum.

Ya yi kira na musamman ga ’yan Majalisar Wakilai da na Majalisar Dokokin Jihar Borno da suka rasa damar sake tsayawa takara, da su karɓi sakamakon a matsayin ƙaddarar Allah, su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyyar.

Gwamnan ya kuma ambaci wani abokin siyasar sa da ya kira da “Ya Massa”, inda ya bayyana shi a matsayin aboki na ƙwarai, tare da kira gare shi da su ci gaba da tafiya tare a rayuwa duk da cewa ba za su riƙe zaɓaɓɓun muƙamai ba.

“Musamman Ya Massa, wanda ya kasance babban abokina. Zai kasance tare da ni mu ci gaba da tafiya tare, tunda ba za mu riƙe zaɓaɓɓun muƙamai ba,” inji shi.

Haka kuma, Zulum ya gargaɗi mambobin sabon kwamitin yaƙin neman zaɓen da aka ƙaddamar, wanda shi ne shugaban kwamitin, da kada su dogara da nasarorin da APC ta samu a zaɓukan baya, sai dai su ɗauki alhakin neman goyon bayan jama’a tun daga tushe.

Ya buƙace su da su koma mazabunsu da rumfunan zaɓensu domin tattaunawa kai tsaye da masu zaɓe, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da wayar da kan jama’a da neman goyon bayansu, maimakon ɗauka cewa nasarorin da aka samu a baya za su tabbatar da nasara a zaɓen 2027.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin samar wa APC gagarumin rinjayen ƙuri’u a Jihar Borno, a matsayin hanyar nuna godiya ga ayyukan raya ƙasa da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa a jihar.

Ya yi kira ga kwamitin yaƙin neman zaɓen da su yi aiki domin ganin dukkan ’yan takarar APC sun samu nasara, tun daga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, har zuwa Mustapha Gubio da sauran ’yan takarar kujerun Majalisar Dokokin Jihar Borno.

By ukarofi

Leave a Reply