Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da tabbatar da riƙon amana a harkokin tattalin arziki da zamantakewa (SERAP) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta bayyana cikakkun bayanai kan shirin tallafin gaggawa da daidaita tattalin arziki na ƙasa (NERSI), wanda ake bai wa waɗanda suka cancanta tallafin kuɗi har Naira 50,000.
A cikin takardar neman bayanai bisa dokar ’yancin samun bayanai, mai ɗauke da kwanan watan 7 ga Nuwamba, 2026, kuma Mataimakin Daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, SERAP ta buƙaci Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, da ya fitar da bayanai kan kuɗaɗen da aka ware wa shirin, yadda ake aiwatar da shi, tsarin zaɓen waɗanda za su amfana, yadda ake biyan kuɗin, yarjejeniyoyin da aka ƙulla da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet, da kuma matakan da za su hana katsalandan na siyasa.
Wannan buƙata ta biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta fitar a ranar 30 ga Oktoba, 2026, inda ta bayyana shirin NERSI a matsayin tallafin kuɗi da aka tanada domin taimaka wa ’yan Nijeriya masu fama da matsin rayuwa. SERAP ta nemi gwamnati ta bayyana adadin kuɗin da aka ware wa shirin a cikin kasafin kuɗi, nawa aka saki domin gudanar da shi, da kuma nawa aka kashe. Haka kuma, ta buƙaci a bayyana ƙa’idojin cancantar samun tallafin, hanyoyin zaɓe da tantance masu cin gajiyarsa, yankunan da shirin ya shafa, da kuma ko naira 50,000 ɗin tallafi ne na sau ɗaya ko kuma ana biyan sa ne duk wata.
ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta gayyaci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC), domin su sa ido kan yadda ake gudanar da shirin tare da binciken zarge-zargen rashawa da ka iya tasowa. A cewar SERAP, “’Yan Nijeriya na da haƙƙin sanin yadda ake kashe kuɗaɗen al’umma da aka ware wa shirin NERSI, waɗanda ke karɓar tallafin, yadda ake zaɓensu, da kuma ko shirin yana isa ga mutanen da suka fi buƙatar taimako.”
ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen fifita magoya bayan siyasa ko rinjayar zaɓin masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027 ba. Ta ce ya kamata a raba duk wani tallafin jinƙai da ake gudanarwa da kuɗaɗen gwamnati bisa ainihin buƙatar mutum da kuma ƙa’idojin cancanta na gaskiya. Ba za a yi amfani da tallafin wajen saka wa magoya bayan siyasa, sayen biyayya ga wata jam’iyya, ɗaukar nauyin gangamin siyasa ko rinjayar ra’ayin masu zaɓe masu rauni ba.
SERAP ta ƙara da cewa, bai kamata a tilasta wa waɗanda za su amfana da tallafin halartar tarukan siyasa, goyon bayan wata jam’iyya ko ɗan takara, rataya ko nuna alamomin siyasa, ko kuma bayyana biyayya ga wani ɗan siyasa a matsayin sharadin samun tallafin ba. Ta jaddada cewa NERSI shiri ne na gwamnati da ake gudanarwa da kuɗaɗen al’umma, ba kyauta ko alherin wani mutum ba.
ƙungiyar ta bayyana cewa fitar da waɗannan bayanai zai bai wa ’yan Nijeriya damar tantance ko ana gudanar da shirin cikin adalci da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa akwai kariya daga rashawa da almundahana. Ta kuma buƙaci Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta samar da bayanan da aka nema tare da ɗaukar matakan da suka dace cikin kwanaki bakwai. SERAP ta yi gargaɗin cewa idan wa’adin ya cika ba tare da ta samu amsa ba, za ta ɗauki matakan shari’a da suka dace.
Haka kuma, ƙungiyar ta ce ta samu rahotannin ƙorafe-orafe daga wasu mutanen da aka sanar cewa sun cancanci tallafin, amma suka kasa karɓar kuɗin. Wasu kuma an sanar da su cewa ba su cancanci samun tallafin ba. Wannan lamari, a cewarta, ya haifar da tambayoyi kan sahihancin tsarin tantance masu cin gajiyar shirin da kuma ingancin hanyoyin biyan kuɗin.
