Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya kare alkawarin bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga dukkan gundumomin siyasa a Jihar Riɓers da suka samu nasarar kai wa Shugaba Bola Tinubu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yilwatda ya bayyana cewa bayar da kuɗin bayan kammala zaɓe ba zai zama sayen ƙuri’a ba, yana mai cewa kyauta ce ta nuna bajinta a harkokin siyasa, ba wani yunƙuri na rinjayar masu zaɓe ba.
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Teleɓision.
Kafin hakan, an ruwaito cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin bayar da Naira miliyan 10 ga kowace gundumar siyasa a Jihar Riɓers da ta kai wa Tinubu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yilwatda ya jaddada cewa bayar da wannan kyauta bayan kammala zaɓe da dukkan matakan shari’a ba zai zama sayen ƙuri’a ba, domin a lokacin an riga an bayyana wanda ya yi nasara.
Ya ce: “Idan aka bayar da kuɗin bayan an kammala zaɓe, an bayyana wanda ya yi nasara, kuma babu sauran wani abu da ake jira, idan kotu ta tabbatar da cewa kun kai wa jam’iyya nasara a gundumarku bisa doka, sannan aka ba ku Naira miliyan 10, ban ga yadda hakan zai zama sayen ƙuri’a ba.”
Sai dai ya bayyana cewa bayar da kuɗin kafin zaɓe da nufin rinjayar masu zaɓe zai zama sayen ƙuri’a.
Ya ƙara da cewa: “Amma idan manufarsa ita ce sayen ƙuri’a, da ya ce zai ba ku Naira miliyan 10 domin ku yi amfani da kuɗin wajen sayen ƙuri’u a ranar zaɓe, domin mutane su zaɓi Shugaba Tinubu. Wannan shi ne sayen ƙuri’a.”
