2027: INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan Atiku, inji Amupitan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar za a ta yi biyayya ga kowane hukuncin kotu kan ko tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar zai iya shiga takarar shugaban ƙasa na 2027 ko kuma akasin haka.

Amupitan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026 a lokacin da yake yi wa wasu ‘yan Nijeriya jawabi a Chatham House da ke Landon, yayin rikicin shari’a kan jagorancin jam’iyyar ADC da sahihancin hanyoyin da aka bi wajen tsayar da Atiku a matsayin ɗan takararta.

A ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026 ne Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya ya soke kwamitin riƙo na jagorancin ADC ƙarƙashin David Mark da hukunce-hukuncensa, ciki har da hanyoyin da aka bi wajen samar da Atiku a matsayin ɗan takara shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Yayin ganawar ta Chatham How, wani wakilan kafar Semaphore Africa ya tambayi Amupitan kan ko za a iya ƙyale Atiku ya shiga takara idan ya gaza yin nasara a shari’a: Shugaban na INEC ya bayar da amsa da cewa hukumar za ta yi biyayya ga kowane umarni da kotu ta bayar, musamman hukuncin Kotun Ƙoli, ba tare da la’akari da tasirin da hakan zai yi ba a siyasance, yana mai kafa hujja da Sashe na 285 da ya hukunta biyayya ga umarnin kotu musamman ta ƙoli.

Haka kuma, Amupitan ya bayyana cewa, INEC tana gudanar da shari’o’i sama da 300 akan siyasa yayin da ya rage saura kwanaki 66 a fara zaɓen 2027. Ya ce, ya taɓa kira da a riƙa warware rikice-rikicen zaɓe watanni shida ko shekara guda kafin zaɓe domin bai wa INEC damar mayar da hankali kan shirye-shiryenta na zaɓuka.

Nafi’u Bala, wanda tsohon shugaban ADC ne na Arewa maso Gabas ne ya shigar da ƙorafin, wanda ya janyo caɓewar rikicin shugabancin jam’iyyar. Tun daga lokacin ne ADC ta shigar ƙorafin ɗaukaka ƙara, wanda ake jiran fitar sakamakonsa ganin cewa har yanzu kotu ba ta yi zama a kai ba.

By Babaji

Leave a Reply