
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara ta sanar da bai wa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu sarautar gargajiya ta “Jagabar Matan Zamfara”.
An yi mata wannan naɗi ne a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026 yayin ziyarar da ta kai wa jihar domin taron gangamin mata na jam’iyyar APC a Arewa maso Yamma da shirin Inganta Mata na jam’iyyar da aka gudanar a Gusau. Mai taimaka wa uwargidan kan harkokin yaɗa labarai, Busola Kukoyi ce sanar da naɗin a ranar Juma’a.
A cewarta, gangamin na Gusau ɓangaren ne na tattara mata da APC ke yi gabanin zaɓukan 2027, yayin da jam’iyyar ke neman tara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu magoya baya domin su sake zaɓar sa a karo na biyu.
Wannan ziyarar ta biyo bayan ayyukan gudanar da tarukan tattara mata da jam’iyyar ke yi a sassan Arewa ta Yamma. Da fari, Cibiyar Tattara Mata ta APC ta kai wa al’umma ziyara a kasuwanni, asibitoci da ƙauyuka a jihar Jigawa a matsayin ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa wa goyon bayan jam’iyyar daga tushe gabanin zaɓukan.
Saidai, sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sa majalisar sarakunan ta ɗauki wannan mataki ba, duk da cewa ana haka ne domin karrama wasu fitattu a cikin al’umma.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan da aka naɗa ɗan Shugaba Bola Tinubu, Seyi Tinubu a matsayin Ɗan Zakin Gwandu da Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Ilyasu Bashar a Jihar Kebbi ya yi masa.
