Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Babbar Kotun Jihar Gombe ta dakatar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga aiwatarwa ko tabbatar da korar Hon. Aliyu Usman Garry daga cikinta har sai an kammala shari’ar da ya shigar yana ƙalubalantar matakin.
Mai Shari’a Daurabo Luka Dalang na sashen kotun da ke Gombe ne ya bayar da umarnin wucin gadi a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, bayan sauraron buƙatar da Garry ya gabatar ta hannun lauyoyinsa.
Kotun ta kuma hana jam’iyyar da shugabanninta ɗaukar duk wani mataki da zai tabbatar da korar Garry da ake zargin an yi a ranar 2 ga Nuwamba, 2026.
Haka kuma, mai shari’ar ya umarci waɗanda ake ƙara da su da su guji duk wani mataki da zai tauye haƙƙin Garry na ci gaba da kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar har sai an kammala shari’ar.
Garry, wanda ke neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027 a ƙarƙashin PDP, ya garzaya kotu ne domin ƙalubalantar matakin korar da ya ce ya saɓa wa ƙa’idojin jam’iyyar da dokokin da suka dace.
Lauyoyinsa, ƙarƙashin jagorancin Eko Ejembi Eko, SAN, tare da Celestina Yauta, sun nemi kotun ta bayar da umarnin wucin gadi domin hana PDP aiwatar da korar har sai an saurari ƙarar gaba ɗaya.
A cikin umarnin, kotun ta kuma buƙaci a gaggauta sauraron ƙarar, tare da ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 24 ga Nuwamba, 2026.
Sai dai umarnin da kotun ta bayar na wucin gadi ne, kuma ba ya nufin ta yanke hukunci na ƙarshe kan sahihancin matakin korar Garry daga PDP.
Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron ɓangarorin biyu a ranar da aka sanya domin ci gaba da shari’ar.
