Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya na neman sabon bashin dala miliyan 500 daga Bankin Duniya domin kafa wani tsarin samar da kuɗaɗen ayyukan more rayuwa, inda ake sa ran amincewa da bashin a ranar 25 ga Mayu, 2027, kwanaki huɗu kacal kafin ƙarshen wa’adin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2027.
Har yanzu ba a amince da bashin ba, amma ranar da aka tsara domin nazari da amincewa da shi ta jawo tambayoyi kan dalilin neman sabon bashin a irin wannan lokaci, da kuma irin tasirin da hakan zai iya yi ga gwamnatin da za ta karɓi mulki.
Bisa ga wani takardar bayanan farko kan aikin da Bankin Duniya ya fitar, wannan bashin wani ɓangare ne na babban shirin samar da kuɗaɗen ayyukan more rayuwa da ya kai dala biliyan 3.85, wanda aka yi wa laƙabi da Nigeria Infrastructure Financing and De-Risking Platform for Growth and Jobs (INFRAGROW).
An tsara wannan shiri ne domin samar da hanyoyin samun kuɗaɗen gudanar da manyan ayyukan more rayuwa tare da rage haɗarin zuba jari, domin bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a Nijeriya. Takardar, wadda aka shirya tare da sabunta ta a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, ta bayyana Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya a matsayin wadda za ta karɓi bashin, yayin da Hukumar Zuba Jari ta ƙasa ta Nijeriya (NSIA) za ta kasance hukumar da ke da alhakin aiwatar da shirin.
Bankin Duniya ya tsara gudanar da bitar fasaha kan yadda za a tsara aikin a ranar 21 ga Janairu, 2027, yayin da aka sanya ranar 25 ga Mayu, 2027 a matsayin lokacin da ake sa ran amincewa da shi. Sai dai bankin ya bayyana cewa wannan jadawali na iya sauyawa, kuma ko da an amince da bashin, hakan ba yana nufin za a fara fitar da kuɗin ko aiwatar da aikin nan take ba. Neman wannan sabon tallafin kuɗi na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara zafi gabanin babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.
Bankin Duniya ya kiyasta cewa Nijeriya na fuskantar gibin kuɗaɗen gudanar da ayyukan more rayuwa da ya kai kusan dala biliyan 100 a duk shekara, yana mai cewa wannan matsala na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziki, ɗorewar harkokin kuɗaɗen gwamnati, gasa a kasuwanni da samar da ayyukan yi.
A cewar takardar, giɓin kuɗaɗen ayyukan more rayuwa a Nijeriya, wanda aka kiyasta ya kai kusan dala biliyan 100 a shekara, na ci gaba da zama babban ƙalubale ga ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Bankin ya bayyana cewa matsalar ba ta tsaya ga ƙarancin jari ko kuɗaɗe kawai ba, domin akwai kuma ƙalubalen shirya manyan ayyukan more rayuwa ta yadda za su iya jan hankalin masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu. Ya ce, domin magance wannan gibi, akwai buƙatar inganta yadda ake tsara ayyuka tun kafin fara aiwatar da su, samar da hanyoyin rage haɗarin zuba jari da kuma yin gyare-gyaren da za su inganta yanayin gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a ƙasar. Bashin dala miliyan 500 da ake nema daga Bankin Duniya ya ƙunshi dala miliyan 400 daga Bankin ƙasa da ƙasa na Sake Ginawa da Bunƙasa (IBRD), da kuma dala miliyan 100 daga ƙungiyar Cigaban ƙasashe ta ƙasa da ƙasa (IDA).
A ɓangaren babban shirin da ya kai dala biliyan 3.85, ana sa ran samun gudunmawar kuɗaɗe daga gwamnati, masu zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu, bankunan kasuwanci da hukumomin da ke bayar da tabbacin biyan basussuka da rage haɗarin zuba jari.
A ƙarƙashin wannan tsari, ana sa ran Hukumar Zuba Jari ta ƙasa ta Nijeriya za ta bayar da dala miliyan 200 a matsayin jarin hannun jari na farko, yayin da masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu su ma za su bayar da wani dala miliyan 200. Haka kuma, ana sa ran samun dala miliyan 600 daga basussukan bankunan kasuwanci, baya ga wasu hanyoyin samar da kuɗaɗe da yarjejeniyoyin bayar da tabbacin zuba jari.
Takardar ta kuma bayyana cewa za a ware dala miliyan 100 daga ƙungiyar Cigaban ƙasashe ta ƙasa da ƙasa domin bayar da tabbacin biyan wasu basussuka, yayin da sauran hukumomin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa za su samar da tabbaci kan zuba jari da ya kai dala biliyan 2.25. Wannan ya sa jimillar kuɗaɗen da za a tanada domin bayar da tabbacin zuba jari ta kai dala biliyan 2.35.
Shirin INFRAGROW zai ƙunshi rassa huɗu masu cin gashin kansu wajen gudanar da ayyukansu, waɗanda kowannensu zai mayar da hankali kan wani babban ƙalubale da ke hana samun jari a fannin ayyukan more rayuwa.
Rukunin farko shi ne Asusun Shirya Ayyuka, wanda zai samar da kuɗaɗen gudanar da binciken yiwuwar aiwatar da ayyuka, tsara yarjejeniyoyin kasuwanci, tantance haɗurran da ke tattare da ayyuka da kuma taimakawa wajen shirya matakan bayar da kwangiloli. Manufar ita ce a samar da ayyukan da za su iya jan hankalin masu zuba jari.
Rukuni na biyu shi ne Asusun Tallafa wa Ayyukan da ke da Gibin Riba, wanda zai taimaka wajen gudanar da muhimman ayyuka ga tattalin arziki da al’umma waɗanda ba sa iya samar da isasshiyar riba ta kasuwanci, musamman idan ana son a ci gaba da sanya kuɗin hidimominsu cikin sauƙi ko kuma a tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnati ke biya sun dore. Bankin Duniya ya ce tsarin bayar da tallafin ta hanyar samar da jari na dindindin zai taimaka wajen kare asalin kuɗaɗen asusun, yayin da za a fi amfani da ribar da jarin ke samarwa wajen tallafa wa ayyukan da ke da giɓin riba.
