Daga AISHA ASAS
A yayin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin ƙarfafa rundunonin tsaron da ke kare iyakokinsu daga hare-haren ‘yan tawaye, wata kotun soji a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta ɗauki matakin da ya jawo hankalin duniya, bayan yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa bisa zargin tserewa daga fagen daga da kuma ƙin bin umarnin manyansu.
Rahoton da kafar DW ta wallafa a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, ya bayyana cewa kotun sojin da ke yankin Walikale, a lardin North Kivu, ta yanke hukuncin ne bayan shafe kwanaki 12 ana shari’ar waɗanda ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban, ciki har da rashin biyayya ga umarni, tayar da ƙayar baya da kuma almubazzaranci da alburusai.
Rahotanni sun nuna cewa an kama akalla sojoji 71 a wasu hare-hare da suka shafi faɗace-faɗace tsakanin dakarun gwamnati da ƙungiyoyin ‘yan tawaye a gabashin ƙasar.
Daga cikin waɗanda aka gurfanar, an yanke wa 66 hukuncin kisa, yayin da aka wanke wasu huɗu, aka kuma yanke wa wani hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.
Matakin ya zo ne a lokacin da rundunar sojin ƙasar ke fuskantar matsaloli wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, musamman a yankunan gabashin ƙasar da ke fama da rikice-rikice.
