‘Yan bindiga sun halaka mai taimaka wa Gwamnan Zamfara a Ƙauran Namoda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindiga sun halaka wani Babban Mai Taimakawa (SSA) ga Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, a wani hari da suka ƙaddamar a garin Ƙauran Namoda, yayin da ‘yan sanda suka ceto mutane 19 da aka sace, waɗanda suka haɗa da mata da yara bayan shafe kwana 22 a hannun ‘yan bindiga.

Rahotanni sun ce, an harbe mataimakin gwamnan mai suna Hon. Nasiru Sani Ƙaura ne a lokacin da maharan suka afka wa yankin Low Cost da ke cikin garin a safiyar ranar Lahadi. Mazauna sun ce, maharan sun kuma farmaki wasu jama’a a lokacin da suke sallar asubahi, inda riƙa harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa zuwa neman mafaka. A yayin haka ne aka halaka, Nasiru, wanda ɗan siyasa ne kuma jagoran al’umma.

Wannan al’amari ya tayar da firgici a Ƙauran Namoda da kuma wasu sassan jihar, inda mutane da dama ke jajentawa tare da bayyana hakan a matsayin babban rashi ga ‘yan yankin. Tuni dai aka gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wannan al’amari ya sabunta damuwa acikin al’umma kan halin tsaro a ƙaramar hukumar da wasu sassan Zamfara ta Arewa, inda ƙauyuka suke cigaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, kashe-kashe da garkuwa da mutane. Akan haka ne mazauna suka kirayi gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su gaggauta faɗaɗa ayyukan bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya, musamman a ƙauyukan da ke fuskantar barazanar hare-hare.

A wani labarin kuwa, Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta yi nasarar ceto wasu mutane guda 19 da aka sace da suka haɗa da mata da yara bayan shafe kwanaki 22 a hannun ‘yan bindiga. An yi awon-gaba da su ne daga ƙauyen Tungar Haki ta yankin Wanke a Ƙaramar Hukumar Gusau, inda aka garzaya da su zuwa wata maɓoya da ke yankin Kungurmi.

Rundunar ta bayyana cewa, an ceto su ne a ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026 da misalin ƙarfe 10 na safe yayin wani atisaye da jami’ansu na reshen yaƙi da ayyukan garkuwa da mutane da ‘yan sandan gidan gwamnatin jihar da jami’an hukumar DSS da kuma wasu mafarauta suka gudanar, kamar yadda kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya bayyana.

By Babaji

Leave a Reply