Ibrahim Masari ya bayyana abin da ya fara shiga tsakaninsa da Gwamna Raɗɗa

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin siyasa, Kabir Ibrahim Masari, wanda kuma makusanci ne ga shugaban ƙasar ya bayyana abin da ya fara janyo saɓani tsakaninsa da gwamnan Katsina Dikko Umar Raɗɗa.

A baya an samu rahotonnin saɓani tsakanin manyan siyasar biyu, lamarin da ya kai ga kama manyan jami’an tsaron gwamnan.

A hirarsa da BBC, Ibrahim Kabir Masara ya bayyana ainihin abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da gwamnan.

Ibrahim Masari, ya ce matsala tsakaninsa da Gwamna Dikko ta faro ne daga zargin rashin son tallata Tinubu a jihar.

”Matsalar ta faro ne daga yaran gwamnan da waɗanda ke aiki da shi, waɗanda ke kafa allunan hotunan tallata gwamnan da yaransa ba tare da saka hotunan shugaban ƙasa ba”, in ji shi.

Masara ya ƙara da cewa hakan bai yi masa daɗi ba shi da wasu ƴan siyasar Katsinan da ke aiki a Abuja, inda suka fara ɗaukar matakin magance hakan.

“Hakan ya sa muka zo ni da Minista da Mallam Jabiru Tsauri waɗanda dukkanmu ma’aikatan shugaban ƙasa ne muka haɗa kuɗi muka yi manyan alluna ɗauke da hotunan Tinubu, muka saka”, in ji shi.

Babban hadimin an Shugaba Tinubu ya ce a jikin allunan da suka kafa sun saka hoton Tinubu da Kashim, Dikko da na tsoffin gwamnonin Katsina biyu, Aminu Bello Masari da Shehu Shema.

Ya ce sauran sun haɗa da nasa da na Muttaqa Rabe da Jabiru.

Ibrahim Masari ya zargi jami’an da ke tsaron lafiyar gwamnan Katsina da jagorantar yaga hotunan Tinubu da ke jikin allunan.

”Sai ya kasance ko da sanin gwamna ko ba saninsa babban dogarinsa da CSO ɗinsa suka jagoranci ƴan banga da suka yi ta yanke hotunan shugaban ƙasa da ke jikin allunan tallen”, in ji shi.

Masari ya ce bai yarda a ce a jihar Katsina ba za a iya tallata Shugaba Tinubu ba.

”Ba a halicci ɗan’adam ɗin da zai ce ba za a iya tallata Tinubu a jihar Katsina ba”, kamar yadda ya bayyana.

Sai dai makusancin na shugaba Tinubu ya yaba wa ayyukan da ya ce Gwamna Raɗɗa ya yi a jihar Katsina a tsawon mulkinsa.

By ukarofi

Leave a Reply