
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Baki ɗaya majalisun dokokin jihohin Nijeriya 36 sun amince da yi wa dokar ƙasa kwaskwarima don kafa ‘yan sandan jihohi, lamarin da ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar amincewa da matakin a dokance karo na ƙarshe.
Magatakardar Majalisar Dokokin Ƙasa, Kamoru Ogunlana ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana ƙudirin a matsayin wanda ya samu amincewa da kaso 100 daga majalisun dokokin jihohin. Amincewar ta kere abin da dokar ƙasa ta hukunta kafin tabbatarwa na samun yardar majalisu 24 ƙarƙashin Sashe na 9(2) na Dokar Ƙasa ta 1999 da aka wa gyara.
Sannan, wannan ci-gaba ya nuna cewa an riga an kammala aikin duba ƙudirin daga ɓangaren majalisun dokokin jihohin bayan makonnin aikin haɗin-gwiwar samar da ‘yan sandan jihohi. Tum a ranar 3 ga Nuwamba ne dai majalisar dokoki ta ƙasa ta sanar da cewa majalisun jihohi 28 sun amince, wanda ya kere biyu bisa uku da doka ta hukunta a samu kafin tabbatarwa.
Kazalika, Ogunlana ya ce an samu jinkirin tabbatarwa daga jagorancin majalisar dokokin ƙasar ne sakamakon buƙatar bayar da damar faɗaɗa shawarwari da samar da daidaito a tsakanin jihohi, yana mai cewa ofishinsa ya kammala aikin gabatar wa Shugaban Ƙasa domin sahalewa.
