Tinubu zai shawarci Antoni Janar kafin sa hannu kan dokar ‘yan sandan jihohi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi ƙudirin gyaran doka na shida (Sixth Alteration Bill), wanda ya bayar da damar samar da ‘yan sandan jihohi a Nijeriya, lamarin da ya kusanto da gyaran dokar ƙasa zuwa matakin ƙaddamarwa a dokance.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya tabbatar da haka a wata takarda da aka fitar a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026 biyo bayan kammala nazari a kai a Majalisar Dokokin Ƙasa ta gudanar.

Gbajabiamila ya ce, masu bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, Sanata Bashir Lado da Wasiu Olanrewaju-Smart ne suka isar wa Tinubu kwafin ƙudirin. A cewarsa, shugaban zai yi nazari a kai tare da shawartar Antoni Janar na Ƙasa, Lateef Fagbemi kan hukunce-hukuncen shari’a kafin amincewa da kuma sanya masa hannu a dokance.

Gbajabiamila, wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban ƙasa akan aikin kafa ‘yan sandan jihohi, ya ce kwamitinsu da kwamitin shawarwarin tsare-tsare, sun gudanar da nazari mai zurfi wajen samar da kwafin ƙudirin na “National Policing Bill”. Ya bayyana cewa, an kuma aike wa Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya domin dubawa da tabbatar da sahihancinsa gabanin aiwatarwa.

A ‘yan kwanakin nan ne dai ƙudirin ya samu amincewar majalisun dokokin jihohi Nijeriya 36, inda hakan ya bai wa shugaban Nijeriya damar da sanya masa hannu a hukumance, kamar yadda Manhaja ta ruwaito.

By Babaji

Leave a Reply