A yau, Nijeriya ta haɗa kai da sauran ƙasashen duniya wajen bikin Ranar Cutar Sukari ta Duniya (WDD) ta bana. ƙungiyar ƙasa da ƙasa Mai Yaƙi da Cutar Sukari (IDF), tare da haɗin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ce ke jagorantar wannan gangami na shekara-shekara. An ƙaddamar da bikin ne a shekarar 1991, sakamakon ƙara nuna damuwa kan yadda cutar sukari ke zama babbar barazana ga lafiyar al’ummar duniya. Taken bikin na bana shi ne, “ɗaukar Matakin Farko Kan Cutar Sukari”. Taken na jaddada muhimmancin gano cutar tun da wuri da kuma fara maganin da ya dace ba tare da ɓata lokaci ba.
Bikin na bana zai mayar da hankali ne kan muhimmancin tabbatar da cewa kowa ya samu damar kula da lafiyarsa idan yana fama da cutar sukari, da kuma buƙatar ɗaukar matakan kare kai daga kamuwa da cutar da kuma matsalolin da take haifarwa. Muhimman abubuwan da ke cikin kulawar masu fama da cutar sun haɗa da samun insulin da sauran magunguna, ilimantar da marasa lafiya da kuma ba su tallafin ƙwararru a fannin lafiyar kwakwalwa. Haka kuma, bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da aka cika shekara 105 da gano sinadarin insulin. Kafin wannan gagarumin bincike, idan aka gano cewa mutum na fama da cutar sukari tamkar yanke masa hukuncin mutuwa ne. Binciken da masana kimiyya, Frederic Banting da Charles Best, suka yi a shekarar 1921 ya ceci rayukan miliyoyin mutane, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a fannin kimiyyar likitanci a wannan zamani.
Mutumin da ke fama da cutar sukari shi ne wanda yawan sukari a jininsa ya haura yadda ya kamata, sakamakon rashin samar da isasshen sinadarin insulin a jikinsa, ko kuma saboda ƙwayoyin halittarsa ba sa amsa aikin sinadarin yadda ya kamata. Bisa ga ƙididdigar da ake da ita, kimanin mutane miliyan 415 ne ke fama da cutar a faɗin duniya, kuma ana hasashen adadin zai kai miliyan 642 nan da shekarar 2040. Kimanin shekaru goma da suka gabata, akwai mutane sama da miliyan 14 da ke fama da cutar a yankin Afirka da ke kudancin hamadar Sahara, kuma ana sa ran adadin zai ninka nan da shekarar 2040.
A halin yanzu, sama da ’yan Nijeriya miliyan bakwai ne ke fama da cutar, amma rabinsu ba su ma san suna ɗauke da ita ba. Abin takaici, rashin sanin halin da suke ciki kan jawo asarar rayukansu. Cutar sukari cuta ce da har yanzu ba a gano maganin da ke warkar da ita gaba ɗaya ba. An rarraba ta zuwa nau’o’i huɗu, wato nau’i na ɗaya, na biyu, na uku da na huɗu, waɗanda ke iya shafar yara, manya da mata masu juna biyu. Masana sun amince cewa ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin shawo kan cutar shi ne amfani da magunguna bisa umarnin likita a kai a kai, tare da cin abinci mai gina jiki da ya dace da yanayin lafiyar mutum.
Cutar sukari, wadda ba ta yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, ta zama ruwan dare a tsakanin matasa da masu tasowa. Ana danganta wannan yanayi, a wani ɓangare, da sauye-sauyen zamantakewa da al’adu cikin sauri da ake samu a ƙasashe masu tasowa, waɗanda suka sa mutane rungumar sababbin salon rayuwa da halaye masu jefa lafiyarsu cikin haɗari. Manyan abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da cutar, waɗanda mutum zai iya kauce musu, sun haɗa da shan taba, rashin cin abinci mai gina jiki, rashin motsa jiki da kuma shan barasa fiye da kima.
Idan ba a gano cutar da wuri ba, ko kuma ba a kula da ita yadda ya kamata ba, tana iya haifar da munanan matsaloli, ciki har da yanke ƙafa ko wani sashe na ƙasan jiki, gazawar ƙoda ta dindindin, hawan jini, lalacewar gani ko makanta, da kuma lalacewar sassan jiki da dama sakamakon toshewar jijiyoyin jini.
Cutar sukari, ko ta gado ce ko kuma wadda mutum ya samu a tsawon rayuwarsa, matsala ce da ke shafar yadda jiki ke sarrafa abinci da makamashin da yake samu daga gare shi. A sakamakon haka, sukari da sitaci ba sa shiga ko sarrafuwa yadda ya kamata, lamarin da kan jawo yawan jin ƙishirwa da fitar da fitsari fiye da kima.
Ba abin mamaki ba ne ganin yadda cutar ta yi ƙamari a tsakanin ’yan Nijeriya, domin har yanzu wayar da kan al’umma game da lafiya bai samu wurin zama ba, hatta a birane da kuma tsakanin mutanen da suka samu ilimi. Talauci mai tsanani ya yi wa mafi yawan ’yan Nijeriya ƙatutu. Bayan shafe tsawon lokaci suna fama da sakamakon mulkin gwamnatocin da ba su yi wa jama’a adalci ba, talakawa sun rasa damar kula da lafiyarsu ta hanyar cin abinci mai kyau da motsa jiki, domin kuwa abin da ya fi gabansu a kullum shi ne neman abin da za su ci da kuma yadda za su tsira.
Abin mamaki kuma shi ne, masu hannu da shuni ma ba su tsira daga barazanar cutar ba. Kamar yadda masana suka bayyana, akwai mutane da dama da ke ɗauke da cutar amma ba su san cewa wata babbar barazana ga lafiyarsu ke ci gaba da bunƙasa a jikinsu ba. Ya kamata ’yan Nijeriya su ɗauki lafiyarsu da muhimmanci. Mutane da dama, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara, ba sa samun damar ganin ƙwararrun likitocin da za su iya gano cutar. Wasu kuma kan danganta rashin lafiyarsu da maita ko asiri, maimakon neman taimakon likita.
Akwai kuma waɗanda ba sa gano cewa suna fama da cutar sai lokacin da ta yi tsanani, inda ko dai ya zama lokaci ya ƙure wajen fara maganin da zai taimaka musu, ko kuma ba su da isassun kuɗaɗlɗen da za su iya biyan kuɗin magani da kula da lafiyarsu.
Shekaru 66 bayan samun ’yancin kai, Nijeriya na ci gaba da jan ƙafa a kusan dukkan ma’aunin da ake amfani da su wajen tantance ci gaban rayuwar al’umma. Cibiyoyin kiwon lafiya da ke birane da ƙauyuka har yanzu ba su da isassun kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata da za su iya kula da cututtuka masu tsanani irin su cutar sukari. Bugu da ƙari, yawan yajin aikin ma’aikatan lafiya ya zama ruwan dare a ɓangaren kiwon lafiya, lamarin da ke tilasta wa waɗanda ke da hali fita ƙasashen waje neman magani. Wasu kuwa sukan faɗa hannun waɗanda ba su da ƙwarewar aikin likitanci, yayin da wasu ke dogaro da hasashe ko kuma shan magunguna ba tare da shawarar likita ba.
Gwamnatoci a dukkan matakai su ne ke da babban nauyin samar wa al’umma ingantaccen tsarin kiwon lafiya da zai wadatar da buƙatunsu. Sai dai yana da muhimmanci ’yan Nijeriya su fahimci cewa motsa jiki a kai a kai, baya ga cin abinci mai gina jiki, na daga cikin muhimman matakan da za su taimaka wajen hana kamuwa da cutar ko rage barazanar ta.
Waɗanda ke da hali ya kamata su yi ƙoƙarin tabbatar da cewa suna cin abinci mai gina jiki da ya ƙunshi nau’o’in abinci daban-daban da jiki ke buƙata. Haka kuma, ya kamata su guji cin abincin banza da yawan shan abubuwan sha masu zaƙi, waɗanda kan ƙara haɗarin ƙiba da yin ƙiba fiye da kima. Baya ga haka, ya dace su mayar da motsa jiki na yau da kullum cikin muhimman abubuwan da suke yi domin kiyaye lafiyarsu.
Duk da waɗannan ƙalubale, akwai abin ƙarfafa gwiwa: mutanen da ke fama da cutar sukari za su iya rayuwa mai tsawo cikin ƙoshin lafiya idan suka kula da kansu yadda ya kamata, suka bi umarnin likitoci, tare da samun kulawa da goyon bayan ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
