Nijeriya na alfaharin karɓar baƙuncin taron ƙasa da ƙasa na hulɗa da jama’a — Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa karɓar baƙuncin Taron ƙasa da ƙasa na Hulɗa da Jama’a na shekarar 2026 (World Public Relations Forum, WPRF) da Nijeriya ta yi, na nuna yadda ƙasashen duniya ke ƙara amincewa da ita, da bunƙasar ƙwarewar ma’aikatanta, da kuma gudummawar da take bayarwa ga harkokin sadarwa a duniya.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron a Abuja, ministan ya ce Nijeriya na alfahari da kasancewa ƙasa ta farko a Yammacin Afirka, kuma ta biyu a nahiyar Afirka da ta karɓi baƙuncin wannan gagarumin taro na duniya.

Idris ya ce: “Zaɓen Nijeriya a matsayin mai masaukin baƙuncin Taron ƙasa da ƙasa na Hulɗa da Jama’a na shekarar 2026 ya nuna cewa ƙungiyar ƙwararrun Hulɗa da Jama’a ta Duniya ta amince da ƙarin ɗaukakar da ƙasarmu take samu a duniya, ƙwarewar da muke da ita da kuma gudummawarmu ga harkokin sadarwa a duniya. Muna alfahari da tarbar wakilai daga sassa daban-daban na duniya domin nuna musu irin abubuwan da Nijeriya take da su.”

Ministan, wanda ya tarbi mahalarta taron a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gode wa Farfesa Justin Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta Hulɗa da Jama’a da Gudanar da Sadarwa (Global Alliance for Public Relations and Communication Management), tare da tawagarsa, bisa amincewa da Nijeriya.

Haka kuma, ya yaba wa Shugaban Cibiyar ƙwararrun Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, da tawagarsa, bisa ƙoƙarin da suka yi na ganin Nijeriya ta samu damar karɓar baƙuncin taron da kuma shirya shi.

Ya ce taken taron na bana, wato “Sadarwa Mai Inganci da ɗaukar Nauyi: Muryar Jama’ar Duniya”, ya zo a daidai lokacin da harkokin sadarwa suke fuskantar ƙalubale sakamakon bunƙasar basirar na’ura mai ƙwaƙwalwa (AI), yaɗa bayanan ƙarya, yaɗa bayanan da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a, da kuma amfani da fasahar zamani wajen murɗe bayanai.

Ya ce: “Dimokiraɗiyya na bunƙasa ne idan ’yan ƙasa suna da ’yancin bayyana ra’ayoyinsu, tambayar masu mulki, samun bayanai da kuma shiga tattaunawar da ta shafi ƙasa. Mun yi imani da cewa dole ne kafafen yaɗa labarai su kasance masu ’yanci domin gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora musu, tare da kiyaye sahihanci, adalci da ƙa’idojin aikin jarida.

“Dole ne sadarwa mai ɗauke da nauyi ta kare gaskiya ba tare da tauye haƙƙin mutane na bayyana ra’ayoyinsu mabambanta ba.”

Idris ya lura da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba da tabbacin ’yancin faɗar albarkacin baki, tare da amincewa da rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen yi wa gwamnati tambayoyi kan ayyukanta.

Ya yi tsokaci kan goyon bayan da Gwamnatin Tarayya take bayarwa wajen kafa Cibiyar ƙasa da ƙasa ta UNESCO mai kula da Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai (IMILI), wadda za ta kasance cibiyar aji na biyu ta UNESCO a Abuja, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ilimin yaɗa labarai da sarrafa bayanai.

Ministan ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai ɗimbin al’adu, fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire, albarkatun ƙasa da haziƙan mutane. Ya ce waƙoƙi, fina-finai, adabi, abinci da kuma ruhin kasuwanci suna daga cikin abubuwan da suka sa ƙasar take samun karɓuwa a idon duniya.

Ya buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da wannan dama wajen gina dangantaka mai ɗorewa, musayar ra’ayoyi da ƙarfafa ƙwarewar sana’ar sadarwa a duniya, tare da sanin al’adu daban-daban da kuma damar da Nijeriya take da su.

Taron ƙasa da ƙasa na Hulɗa da Jama’a na shekarar 2026 ya haɗa ƙwararru a fannin hulɗa da jama’a da sadarwa daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna rawar da sadarwa mai ɗaukar nauyi za ta taka wajen magance ƙalubalen duniya da kuma ƙarfafa wannan sana’a.

By ukarofi

Leave a Reply