Daga RABI’U SANUSI a Kano
MAGGI, ɗaya daga cikin manyan sinadaran kayan ɗanɗano a Najeriya, ya yi bikin cika shekaru 60 yana ƙara armashi ga abincin ‘yan Najeriya ta hanyar ƙaddamar da gangamin bikin cika shekarun.
Bikin, wanda aka yi wa lakabi da Maggi-nificent@60, an tsara shi ne domin tunawa da shekaru 60 na cin abinci tare, bunƙasa al’adun iyali da kuma tabbatar da lokuta masu daɗi a ɗakunan girki a faɗin ƙasar.
An ƙaddamar da wannan gangami ne a hukumance a wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, 2026, inda shugabannin kamfanin Nestlé Nigeria Plc suka waiwayi tafiyar da Maggi ya yi tsawon shekaru tare da bayyana shirye-shiryen da za su yi domin murnar wannan babban tarihi tare da masu amfani da kayayyakinta a faɗin ƙasa.
Gangamin dai ya karrama ’yan Najeriya da suka mayar da MAGGI wani ɓangare na girkinsu na yau da kullum, tun daga girke-girken gargajiya na iyali zuwa abincin bukukuwa da sauran lokuta na musamman.
Da yake magana a taron, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Nestlé Nigeria Plc, Wassim Elhusseini, ya ce muhimmancin wannan biki ya wuce tsawon shekarun da sinadarin ya yi a kasuwa, ya ma shafi amincewar da ya samu daga masu amfani da shi a tsawon shekaru.
Ya ce: “Tsawon shekaru 60 MAGGI ya kasance wani ɓangare na ɗakunan girkin ’yan Najeriya, abincinsu da kuma abubuwan tunawarsu. Tarihi ba kawai tsawon shekaru ba ne. Yana nufin samun amincewa a hankali cikin lokaci tare da ci gaba da sauyawa daidai da buƙatun mutanen da ya ke yi wa hidima.”
A matsayin wani ɓangare na bikin, MAGGI ya kuma ƙaddamar da wata gasa ta ƙasa baki ɗaya mai suna ‘Text & Win’, wadda ke bai wa abokan hulda damar lashe motocin alfarma kirar SUV guda 12, kyautar Naira miliyan 1 ga mutane 60, tare da sauran kyaututtukan kuɗi, kayan amfani na gida da sauran kyaututtuka masu ƙayatarwa.
Wannan gasa ta fara ne ranar 1 ga watan Nuwamba kuma za ta ci gaba har zuwa 31 ga watan Disamban 2026. A halin yanzu ana gudanar da ita, kuma masu amfani da sinadarin na ci gaba da shiga yayin da ake samun waɗanda ke yi nasara a cikin ta.
A cewar manajar rukunin kayan girki ta Nestlé, Funmi Osineye, bikin wata dama ce ta nuna godiya ga mutanen da suka taka rawa wajen nasarar sinadarin tsawon shekaru.
Ta ce: “Ko da yake MAGGI ne ke bikin cika shekaru 60, mun san cewa nasarar shi ta kasance kan wani abu da ya fi sinadarin kansa girma. Nasarar ta shafi mutane ne.”
Ta kuma ce bikin ya haɗa da abokan hulɗar kasuwanci, inda aka ba manyan masu rarraba kayayyakin MAGGI guda 15 kyautar kujerar tafiya zuwa birnin Alkahira na ƙasar Masar tare da biyan dukkan kuɗaɗen tafiyar, domin karrama jajircewarsu da goyon bayansu ga sinadarin tsawon lokaci.
Ga masu buƙatar shiga gasar, ana buƙatar masu amfani da sinadarin su sayi fakitin MAGGI Star ko MAGGI Chicken da aka yi wa alamar gasa ta musamman, su cire lambar sirri da ke cikinta, sannan su shigar da ita ta hanyar lambar USSD ta 80113#, ko kuma su duba QR Code da ke jikin fakitin.
Baya ga kyaututtukan, gangamin na MAGGI-nificent@60 da saƙonsa na “Me & MAGGI… Sooo Good Together” na bikin abubuwan tunawa, al’adun girki da kuma jin dadin kasancewa tare tsawon lokaci, waɗanda suka haɗa iyalai masu yawa a Najeriya ta hanyar abinci mai gamsarwa tsawon shekaru.
Yayin da MAGGI ke bikin wannan babban tarihi, sinadarin ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na daddadan abinci da ke sauyawa a Najeriya, tare da yaba wa masu amfani da shi da ma sauran abokan hulɗa da suka taimaka wajen dorewar tafiyar a cikin shekaru 60 da suka gabata.
