Kotu ta yi watsi da ƙarar Sheikh Ibrahim Khalil kan takarar Gwamnan Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi watsi da ƙarar da fitaccen malamin addini, Sheikh Ibrahim Khalil, ya shigar yana neman a maye gurbin Alhaji Ibrahim Ali Amin, wanda aka fi sani da Little, a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADC.

Mai Shari’a SM Shuaibu ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, bayan ya tabbatar da cewa ƙarar ta wuce wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada. Haka kuma, mai ƙarar ya kasa tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 22 ga Mayun 2026.

Alƙalin ya ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ba ta sa ido kan zaɓen fidda gwani kamar yadda doka ta tanada, domin wasiƙar gayyatarta ta fito ne daga reshen jam’iyyar na jihar, maimakon kwamitin gudanarwarta na ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa wa’adin shigar da ƙarar ya fara ne a watan Agusta, lokacin da INEC ta karɓi sunan Little, ba a watan Satumba ba, lokacin da Sheikh Ibrahim Khalil ya samu labarin miƙa sunan.

Ya ce bisa sashe na 289 na Dokar Zaɓe, wa’adin shigar da ƙara yana farawa ne daga lokacin da abin da ake ƙalubalanta ya faru. Saboda haka, ƙarar Malam Ibrahim Khalil ta wuce wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada.

Haka kuma, alƙalin ya ce Sheikh Ibrahim Khalil bai gabatar da hujjar da za ta tabbatar da cewa ya lashe zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 22 ga Mayun 2026 ba.

Tun da farko, kotun ta amince cewa Sheikh Ibrahim Khalil na da ikon shigar da ƙara domin ƙalubalantar zaɓen fidda gwani idan yana ganin an saɓa wa wata ƙa’ida wajen zaɓen ɗan takarar jam’iyyar.

Sai dai a ƙarshe, bayan nazarin hujjojin da aka gabatar, kotun ta bayyana cewa ƙarar ba ta da tushe, kuma an shigar da ita ne bayan wa’adin da doka ta tanada. Saboda haka, ta yi watsi da ita.

By ukarofi

Leave a Reply