Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi zargin cewa tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya fara sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne bayan buƙatar da ya gabatar wa shugaban ƙasar na ya mara wa ’yarsa, Iyabo Obasanjo, baya domin ta zama gwamnan Jihar Ogun ta ci tura.
Fayose ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da gidan talabijin na TVC, inda yake mayar da martani kan sukar da ake yi wa gwamnatin Tinubu, musamman ikirarin Obasanjo cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaban ƙasar ya kawo sun jefa ’yan Nijeriya cikin talauci da kashi 300 cikin 100.
Da yake amsa tambaya kan lamarin, tsohon gwamnan ya bayyana Obasanjo a matsayin mutumin da ake ɗaukaka darajarsa fiye da kima, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar na da ɗabi’ar sukar shugabannin da suka gaje shi da kuma neman jan hankalin jama’a ta hanyar sukar wasu.
Fayose ya ce Obasanjo ya taɓa sukar gwamnatocin tsoffin shugabannin ƙasa, Umaru Musa Yar’Adua da Goodluck Jonathan.
“Mun fiye ɗaukaka darajar Obasanjo fiye da kima. Wannan shi ne gaskiya. Hanya ce tasa. A rayuwa, babu wanda ya fi Obasanjo iya wannan salon. Idan wani zai yi magana, ko dai Obasanjo ne ko kuma babu wani,” inji Fayose.
Ya ƙara da cewa Obasanjo na neman kulawar jama’a kuma ba ya ganin alheri a cikin kowa.
Ya ce: “Idan ka dubi Obasanjo, ya soki Yar’Adua da Jonathan. A zahiri, ya mayar da kansa maƙiyin Jonathan. Da zarar ba a biya masa buƙatarsa ta samun izini daga gare shi a kan al’amura na yau da kullum ba, Obasanjo kan shiga damuwa.”
Fayose ya kuma tuna cewa a watan Afrilun 2026, Obasanjo na cikin waɗanda suka tarbi Shugaba Tinubu a Jihar Ogun yayin ƙaddamar da filin jirgin saman Gateway International Cargo Airport.
Ya ce a lokacin, tsohon shugaban ƙasar ya sanya kaya masu kama da na Tinubu, sannan ya yi masa yabo.
Sai dai Fayose ya yi zargin cewa Obasanjo ya tuntuɓi tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba, domin ya taimaka masa wajen shawo kan Tinubu ya mara wa burin ’yarsa, Iyabo Obasanjo, na zama gwamnar Ogun baya.
“Kun san Iyabo Obasanjo, ’yar Obasanjo. Obasanjo ya je wurin Cif Aremo Olusegun Osoba ya roƙe shi da ya taimaka masa ya roƙi Tinubu domin Iyabo Obasanjo ta zama gwamnar Jihar Ogun,” inji shi.
Ya ƙara da cewa: “Wannan ne dalilin da ya sa Obasanjo ya je tarbar Shugaba Tinubu.
“Da zarar wannan buƙata ta ci tura, sai Obasanjo ya tuna da abin da Osoba ya rubuta game da shi a littafinsa, sannan ya mayar masa da martani saboda abin da yake nema bai samu ba.
“Yana zuwa yana roƙo a bayan fage, idan kuma bai samu abin da yake so ba, sai ya fara kai hari gare ka.”
Rahoton ya bayyana cewa kalaman Fayose sun zo ne a daidai lokacin da dangantakarsa da Obasanjo ta daɗe tana cikin saɓani, inda sukan yi musayar zarge-zarge da kalamai masu zafi a kafafen yaɗa labarai tsawon kusan shekaru goma.
A halin da ake ciki, Iyabo Obasanjo na daga cikin waɗanda suka nuna sha’awar neman tikitin takarar gwamnan Jihar Ogun a ƙarƙashin jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen 2027.
A watan Fabrairun 2026, ta bayyana aniyarta ta shiga takarar, amma daga bisani ta dakatar da burinta bayan jam’iyyar ta amince da Sanata Solomon Adeola a matsayin ɗan takararta na masalaha.
