‘Yan bindiga sun halaka basarake da wasu, sun babbake ƙauye a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ‘yan bindiga a Jihar Neja, sun halaka Mai Garin ƙauyen Luman Basle da wasu adadi na mutane a Ƙaramar Hukumar Borgu.

An ce ‘yan bindigar sun afka wa ƙauyen, mai nisan wani ƙaramin adadin kilomita daga garin Luma a ƙaramar hukumar ne a safiyar yau Asabar da misalin ƙarfe 5 na asubahi.

Wani mazauni da ya zanta da ‘yan jarida, ya ce an halaka mutane da dama ciki har da mai garin, inda ya ƙara da cewa sun cinna wa ƙauyen wuta gabanin su tsere. Ya ce, mutane da dama sun tsere zuwa bayan gari a lokacin da maharan suka afka wa yankin domin neman mafaka, saidai ba a san ainihin adadin waɗanda aka kashe ba amma ya ce suna da yawa.

Ya kuma yi iƙirarin cewa, wasu daga cikin maharan yaran Fulani ne da suka haɗe da ‘yan bindiga kafin suka aiwatar da mummunan aikin nasu.

Saidai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Neja ba ta fitar da wani saƙo ba a kai.

By Babaji

Leave a Reply