“Zan iya kwana a kan shimfiɗar laka kamar yadda zan iya kwana a kan shimfiɗar alfarma”
Daga AISHA ASAS
Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja, inda muke haska rayuwar mata, mu waiwayi tafiyarsu, mu kalli ƙalubalen da suka fuskanta, mu kuma nazarci darussan da za a iya ɗauka daga abubuwan da suka faru da su. Domin a rayuwa, ba nasara kaɗai ce ke ba da labarin mutum ba; a wasu lokuta, yadda mutum ya fuskanci ƙalubale da kuma yadda ya bi hanyoyin da suka dace wajen warware su kan bayyana wasu muhimman ɓangarori na rayuwarsa.
Akwai matan da sunayensu suka shahara saboda muƙaman da suka riƙe, akwai waɗanda aka san su saboda gudunmawar da suka bayar ga al’umma, sannan akwai waɗanda tarihin rayuwarsu ya zama wani ɓangare na tarihin ƙasarsu da nahiyarsu baki ɗaya. Amma idan aka waiwayi rayuwar wasu daga cikin waɗannan mata, za a fahimci cewa hanyar zuwa nasara ba koyaushe take shimfiɗe da wardi ba. Wani lokaci tana farawa ne da talauci da rashin tabbas, asara da kuma fuskantar yanayin da mutum ba zai taɓa mantawa da shi ba.
Irin wannan tafiya ce ke tattare da rayuwar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, masaniyar tattalin arziki ’yar Najeriya wadda ta yi aiki a manyan cibiyoyin duniya, ta jagoranci muhimman sauye-sauye a ƙasarta, sannan ta shiga tarihin duniya a matsayin mace ta farko kuma Ba’afirka ta farko da ta zama Darakta-Janar ta ƙungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO). A yau, tana jagorantar wannan ƙungiya a zangonta na biyu, amma kafin ta kai wannan matsayi, akwai tarihin yarinya da ta ga illar yaƙi da yunwa da idanunta, wata ɗaliba da ta nemi ilimi a ƙasashen waje, da kuma mace da ta fuskanci barazana a lokacin da take ƙoƙarin sauya wasu hanyoyin tafiyar da kuɗin ƙasarta.
To, wace ce Ngozi Okonjo-Iweala? Wane irin gida ta taso a ciki, kuma wace hanya ta bi kafin ta zama ɗaya daga cikin matan da ake sauraron ra’ayinsu a fagen tattalin arzikin duniya?
Shin wace ce Ngozi Okonjo-Iweala, kuma daga ina ta fito?
An haifi Ngozi Okonjo-Iweala a ranar 13 ga Yuni, 1954, a garin Ogwashi-Uku da ke Jihar Delta a Najeriya. Ta fito daga gida mai kusanci da ilimi, domin mahaifinta, Farfesa Chukuka Okonjo, masani ne a fannin tattalin arziki, yayin da mahaifiyarta, Kamene Okonjo, ita ma ta kasance malamar jami’a. Mahaifinta kuma yana da sarautar gargajiya ta Obi na Ogwashi-Uku.
A farkon rayuwarta, Ngozi ta yi zaman ƙuruciya tare da kakarta, Dora, a ƙauye. A wannan lokacin ta koyi wasu ayyukan yau da kullum da suka haɗa da debo ruwa, tara itace da taimaka wa kakarta a aikin gona. Iyayenta sun kasance suna karatu a ƙasar waje, saboda haka ba ta rayu tare da su a farkon shekarunta ba. Daga baya, lokacin da iyayenta suka dawo Najeriya, ta koma makarantar da ke kusa da inda suke aiki.
Wannan rayuwa ta ƙuruciya ta ba ta damar sanin yadda ake rayuwa a karkara, amma babban abin da ya sauya tafiyarta ya faru ne a shekarar 1967, lokacin da Yaƙin Basasar Najeriya ya ɓarke. A lokacin tana kusan shekara 13, kuma rikicin ya shafi iyalinsu kai tsaye. Mahaifinta ya shiga aikin rundunar Biafra, yayin da ita da sauran ‘yan uwa suka fuskanci ƙaura da matsin rayuwa. Iyalin sun rasa gida da dukiyoyinsu, kuma a wasu lokuta suna fama da ƙarancin abinci.
A wata hira da jaridar The Washington Post ta yi da ita, ta bayyana cewa lokacin da yaƙin ya ƙare a shekarar 1970, mahaifinta ya tambayi ‘ya’yansa abin da suka rage musu bayan asarar da suka yi. Amsar da ta bayar ita ce, ba su da komai. Sai mahaifinta ya tunatar da su cewa duk da sun rasa dukiyoyinsu, suna da kawunansu da kwakwalwarsu, kuma za su iya sake farawa da abin da ke hannunsu. Wannan magana ta zama ɗaya daga cikin muhimman darussan da ta riƙe daga mahaifinta.
Ta yaya yarinyar da ta fuskanci ƙuncin yaƙi ta samu damar karatu a Harɓard da MIT?
Bayan yaƙin ya ƙare, iyalinsu suka fara sake gina rayuwarsu. A wannan lokacin, ilimi ya kasance ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da iyayenta suka ƙarfafa a cikin ‘ya’yansu. Ngozi ta ci gaba da karatu, har ta samu damar tafiya Amurka domin neman ilimi. A shekarar 1977 ta kammala karatun tattalin arziki a Jami’ar Harɓard, inda ta samu sakamakon magna cum laude, wanda ke nuna babban matakin ƙwarewa a karatu.
Daga nan ta ci gaba da karatu a Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (MIT), inda ta samu digirin digirgir a fannin tattalin arzikin yankuna da bunƙasa tattalin arziki a shekarar 1981. Wannan fanni ya dace da irin abubuwan da ta gani tun tana ƙarama, domin ta taso a ƙasar da ke fuskantar matsalolin talauci, rashin daidaito da kuma buƙatar samar da hanyoyin da za su inganta rayuwar jama’a.
Amma abin da ya kamata a fahimta shi ne, karatun da ta yi bai kasance kawai hanyar samun takardar shaidar ilimi ba. Ya ba ta kayan aikin fahimtar yadda tattalin arzikin ƙasa ke aiki, dalilin da ya sa wasu ƙasashe ke samun ci gaba yayin da wasu ke ci gaba da fama da matsaloli, da kuma yadda manufofin gwamnati kan shafi rayuwar talakawa. Daga nan ne tafiyarta ta shiga wani sabon mataki, inda ta fara amfani da iliminta a manyan cibiyoyin duniya.
Wane aiki ta fara yi bayan kammala karatunta?
A shekarar 1982, Ngozi ta shiga aikin Bankin Duniya, babbar cibiyar kuɗi da ke taimaka wa ƙasashe wajen gudanar da ayyukan ci gaba da magance matsalolin tattalin arziki. Ta shafe shekaru 25 tana aiki a wannan banki, inda ta fara a matsayin masaniyar tattalin arzikin ci gaba, daga bisani ta samu manyan muƙamai har ta zama Manajan Darakta mai kula da ayyuka, matsayi na biyu mafi girma a tsarin shugabancin bankin.
A wannan muƙami, ta kula da ayyukan da suka kai darajar dala biliyan 81 a yankuna daban-daban, ciki har da Afirka, Kudancin Asiya, Turai da Asiya ta Tsakiya. Aikin ya ƙunshi hulɗa da gwamnatoci, tattaunawa kan manufofin tattalin arziki, da kuma tsara hanyoyin tallafa wa ƙasashen da ke fama da matsalolin ci gaba.
A shekarar 2010, ta jagoranci ƙoƙarin Bankin Duniya na tara dala biliyan 49.3 a matsayin tallafi da lamuni mai sauƙin sharadi ga ƙasashe mafi ƙarancin kuɗi. Wannan aiki ya ƙara tabbatar da matsayinta a matsayin ƙwararriyar masaniya a fannin tattalin arzikin ci gaba, tare da ba ta gogewar hulɗa da shugabannin ƙasashe da masu tsara manufofi a sassa daban-daban na duniya.
Duk da wannan nasara, Ngozi ba ta manta da ƙasarta ba. A shekarar 2003 ta amince ta dawo Najeriya domin shiga aikin gwamnati, a lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin bashi da kuma tambayoyi masu yawa game da yadda ake tafiyar da kuɗaɗen jama’a. Wannan mataki ya nuna cewa burinta bai tsaya ga samun babban matsayi a ƙasashen waje ba; ta kuma so ta yi amfani da ƙwarewarta wajen taimaka wa ƙasarta.
Me ya sa aka naɗa ta ministar kuɗi, kuma wace nasara ta fara samu?
A shekarar 2003, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya naɗa Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin ministar kuɗi. Wannan naɗi ya sanya ta zama mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami a Najeriya. A lokacin, ƙasar tana da babban nauyin bashi, kuma akwai buƙatar sake duba yadda ake tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da kuma yadda ake amfani da kuɗin shiga daga albarkatun ƙasa.
ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ta jagoranta shi ne tattaunawar Najeriya da ƙungiyar ƙasashen da ake kira Paris Club, waɗanda ƙasar ke bin bashi. Tattaunawar ta kai ga kawar da bashin da ya kai dala biliyan 30, ciki har da soke dala biliyan 18. Wannan nasara ta kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake danganta wa aikinta a ma’aikatar kuɗi.
Haka kuma, ta yi ƙoƙarin samar da tsarin da zai sa jama’a su riƙa samun bayanai game da kuɗaɗen da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ke samu daga rabon kuɗin tarayya. A wata hira da The Washington Post, ta bayyana cewa an fara wallafa bayanan kuɗaɗen shiga a jaridu, domin jama’a su san adadin kuɗin da kowace hukuma ke samu, su kuma iya tambayar dalilin da ya sa ba a ganin wasu ayyuka a yankunansu.
Wannan mataki ya taimaka wajen ƙara buɗe tattaunawa kan riƙon amana da yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a. Sai dai irin waɗannan sauye-sauye ba koyaushe suke zuwa ba tare da turjiya ba, musamman idan sun shafi hanyoyin da wasu suka saba cin moriya daga gare su.
Shin ta taɓa zama ministar harkokin wajen Najeriya?
Eh. A shekarar 2006, Ngozi ta taɓa riƙe muƙamin ministar harkokin wajen Najeriya na ɗan lokaci. Ta zama mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami, bayan ta riga ta kafa tarihi a ma’aikatar kuɗi. Daga baya ta koma Bankin Duniya, inda ta ci gaba da aikinta har zuwa shekarar 2011.
A wannan shekarar ce ta sake dawowa Najeriya domin zama ministar kuɗi a karo na biyu, tare da riƙe matsayin mai kula da daidaita harkokin tattalin arzikin ƙasa a gwamnatin Goodluck Jonathan. Wannan karo na biyu ya zo da ƙalubale masu yawa, domin ƙasar tana fama da matsalar yadda ake sarrafa kuɗin shiga daga man fetur, batun tallafin man fetur da kuma zarge-zargen almundahana a wasu sassan harkokin gwamnati.
A wannan zangon ne aka aiwatar da wasu tsare-tsare da suka shafi yadda ake karɓa da sarrafa kuɗaɗen gwamnati, ciki har da Asusun Bai ɗaya (Treasury Single Account), wanda manufarsa ita ce tattara kuɗaɗen hukumomin gwamnati a tsarin asusu guda domin ƙara sa ido da gaskiya. Sai dai, kamar sauran manufofin tattalin arziki, wasu matakan da aka ɗauka a lokacin sun haifar da muhawara da suka daga wasu ɓangarori na al’umma.
Don haka, ba za a iya kallon tarihin aikinta a gwamnati a matsayin jerin nasarori marasa ƙalubale ba. Akwai manufofin da aka yaba, akwai waɗanda aka soki, kuma akwai batutuwan da suka ci gaba da zama abin tattaunawa a Najeriya. Fahimtar wannan ɓangare yana da muhimmanci domin labarin Gimbiya ba ya buƙatar a nuna ta a matsayin mutum marar kuskure, sai dai a fahimci irin nauyin da ke tattare da muƙaman da ta riƙe da kuma sakamakon manufofin da aka aiwatar.
Wane ƙalubale ne ya kai ga sace mahaifiyarta?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardar Allah.
