Sojoji sun kashe ‘yan bindiga tare da rushe maɓoyarsu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Dakarun 17 Brigade na rundunar sojin Najeriya, ƙarƙashin Operation FANSAN YANMA, sun ƙara ƙaimi a hare-haren da suke kai wa ’yan ta’adda a Jihar Katsina, inda suka kashe ’yan ta’adda uku da ake zargi tare da ƙwato babura da kayan aiki, tare da rushe maɓoyar su a ƙananan hukumomin Sabuwa, Musawa da Malumfashi.

Ayyukan da aka gudanar sun nuna ƙudurin sojojin na korar ’yan ta’adda, hana su mafaka da dawo da zaman lafiya a al’ummomin da fashi da laifukan tashin hankali suka shafa.

Dakarun sojoji na Combat Team 3, tare da goyon bayan 17 Brigade Strike Force, sun kai hari kan maɓoyar ’yan ta’adda a gefen ƙauyen Madachi da ke Sabuwa. Dakarun sun gamu da tirjiya daga ‘yan bindigan, amma sun mayar da martani da ƙarfin wuta mai rinjaye, inda suka kashe ’yan ta’adda uku, suka ƙwato babura. Sai dai ba a samu asarar rai ba a ɓangaren sojoji.

Haka kuma dakarun 83 Battalion tare da jami’an Forward Operating Bases da ke Malumfashi da mafarauta na gida, sun gudanar da sintiri zuwa ƙauyen Tsabe da ke Musawa da Tsamiyan Maigoro da ke Malumfashi, biyo bayan bayanan sirri kan ayyukan shahararren shugaban ’yan ta’adda, Rabe Rajaja.

Dakarun sun yi arangama da ’yan ta’addan a wani gari da aka yi watsi da shi, inda suka tilasta musu gudu da raunukan harbin bindiga, yayin da suka yi watsi da baburan da aka ƙwato.

Sojojin sun ce suna cigaba da matsin lamba kan ’yan ta’adda ta hanyar faɗaɗa ayyukan sharewa a kusa da dazukan Madachi, Dungun Muazu da Dankolo da ke Sabuwa, ta hanyar hare-hare na asuba, harbin bindigogi masu nauyi kan sansanonin ’yan ta’adda da kuma tura dakarun toshe hanya a kan hanyoyin tserewa.

A halin da ake ciki, kwamandan 17 Brigade, Birgediya Janar Ishaya Ibrahim, ya kai ziyarar tantance aiki zuwa Forward Operating Bases da ke Mabai da Faskari don tantance shirye-shiryen yaƙi, ingancen aiki da jin daɗin sojoji.

A yayin ziyarar, ya karɓi bayanan aiki, ya duba kayan aiki, ya ƙarfafa sojoji da su ci gaba da ladabi da nuna ƙwarewa, tare da magance batutuwan ƙarin girma, kayan sawa da kayan soji. A FOB Faskari, ya gana da mafarauta da ’yan banga, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da bayar da ingantattun bayanan sirri da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.

Ya kuma ziyarci sojojin da aka tura a Machika don tantance shirye-shiryen aikinsu, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙara ƙarfin Brigade na magance barazanar tsaro a yankin.

A cikin sanarwar da aka fitar muƙaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na soji na 17 Brigade, Kyaftin Abayomi Adisa, ya ce dakarun Operation FANSAN YANMA sun ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da ayyukan kai hari kan ’yan ta’adda ta hanyar ayyukan da suka dogara da bayanan sirri da ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki na tsaro, tare da sake tabbatar da ƙudurin sojojin na dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Katsina da Arewa maso Yamma gaba ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply