Mata a Zamfara sun nuna goyon bayansu ga Marafa a ƙarƙashin NDC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Dubban mata daga ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara sun yi taron gangami domin bayyana goyon bayansu ga Sanata Kabir Garba Marafa a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin Jam’iyyar NDC.

Taron, wanda aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar, ya kasance bikin ƙaddamar da Marafa Amazons for Change, wata sabuwar ƙungiyar mata da Modibbo Aminu ya kafa.

Marafa Amazons for Change wata ƙungiya ce mai ƙarfi da ta ƙunshi matasa mata, masu ilimi, da mata ‘yan kasuwa waɗanda suka haɗa kai da manufa ɗaya, watau ceto Jihar Zamfara da tabbatar da sabon shugabanci a shekarar 2027.

Da take jawabi a wajen taron, Shugabar matan Hajiya Sadiya Salisu, ta bayyana gwamnatin yanzu ta Gwamna Dauda Lawal a matsayin gwamnati da ta gaza tana mai nuna gazawarta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Ta koka da cewa mata da dama sun zama zawarawa sakamakon rashin tsaro, yayin da mazajensu da ‘yan uwansu suka zama mabaratan ƙarfi da yaji

Hajiya Sadiya ta bayyana cewa zaɓen Sanata Kabir Garba Marafa wajibi ne a gare su, tana mai alwashin ci gaba da wayar da kan al’umma daga tushe domin tabbatar da nasarar Sanatan.

Taron, wanda aka gudanar cikin lumana, ya samu halartar mata da ‘yan mata marasa adadi inda suka ƙuduri aniyar bayar da gudummawarsu domin kayar da gwamnatin yanzu.

Hajiya Sadiya ta bayyana gwamnatin Dauda Lawal a matsayin gwamnatin da ta gaza tabbatar da makomar ‘yan Zamfara, kuma ta yi alƙawarin cewa ƙungiyar za ta yi amfani da ƙuri’unsu wajen korar gwamnatin a zaɓe mai zuwa.

“Za mu wayar da kai daga gida zuwa gida, daga mazaba zuwa mazaba, daga kasuwa zuwa kasuwa, har sai Marafa ya zama Gwamna,” Cewar Hajiya Sadiya.

A cewarta, kasancewar Modibbo Aminu ya samu nasarar kafa ƙungiyoyi biyu daban-daban masu ƙarfi, Marafa Ambassadors for Change da Marafa Amazons for Change, hakan ya nuna ƙarfinsa na jagoranci da haɗa kan masu ilimi a faɗin jihar.

Ƙungiyoyin biyu, a cewarta, suna da karfi da ikon kai Zamfara ga Sanata Kabir Garba Marafa a 2027.

Ƙungiyar ta kuma yaba da gudummawa mai matuƙar amfani ta Abba Garba, wanda ƙoƙarin sa ga wannan tafiya ba za a iya misalta shi ba.

Hajiya Sadiya ta yi kira ga dukkan masu ilimi da mata masu kishi a faɗin Jihar Zamfara da su shiga wannan tafiya, tana mai bayyana ta a matsayin tafiya da za ta yiwa kowa adalci.

Ta ce Marafa Ambassadors for Change da Marafa Amazons for Change ba kungiyoyi na yau da kullum ba ne, illa manyan dakaru masu ilimi da cikakken tsari da shirye-shirye masu ma’ana domin ceto Jihar Zamfara.

Sanata Marafa, a cewar ta, shi ne dan siyasa daya tilo a Zamfara da ke da gaskiya, ƙwazo da hangen nesa kuma shugaban da ba ya ƙarya, ba ya yaudara, kuma ba ya cin amanar mutanensa.

By ukarofi

Leave a Reply