Daga UMAR GARBA a Katsina
Dandalin sada zumunta na Instagram ya cire wani bidiyo da ya yaɗu sosai, wanda wata mata ‘yar ƙasar waje mai yawon buɗe ido ta wallafa, inda take zargin Sarkin Daura da ke Jihar Katsina, Alhaji Faruk Umar Faruk, da cin zarafinta a lokacin da ta kai ziyara fadarsa.
Matar ta wallafa bidiyon ne a shafinta na Instagram mai suna @beduinqa, inda ta bayyana abin da ta ce ya faru a lokacin ziyarar ta a fadar Sarkin.
Sai dai binciken da aka gudanar a safiyar Litinin ya nuna cewa an cire bidiyon daga shafin, lamarin da ya jawo tambayoyi kan dalilin cire shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Instagram na iya cirewa ko toshe bidiyo idan aka samu zargin cewa abubuwan da ke cikinsa sun sava wa ƙa’idojin amfani da dandalin, dokokin haƙƙin mallaka ko wasu manufofinsa.
Zargin da matar ta yi wa Sarkin Daura ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.
