Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe
Rikicin shugabanci a jam’iyyar Labour Party (LP) a Jihar Gombe ya ƙara ɗaukar sabon salo, yayin da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a zaɓen 2027, AIG Zubair Halilu Mu’azu (mai ritaya), ya buƙaci Alhaji Mohammed Jibrin Barde da ya daina ikirarin shugabancin jam’iyyar a jihar.
Mu’azu ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar na ƙasa da su gaggauta shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin da ya ce yana barazanar raba kan mambobin jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Talata a Gombe, inda ya zargi Barde da ƙoƙarin karɓe ragamar shugabancin jam’iyyar ba tare da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ta ba.
A cewarsa, rikicin ya samo asali ne bayan ficewar zaɓaɓɓen shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Ezra Jatau, zuwa jam’iyyar PDP, lamarin da ya haifar da gurbin shugabanci da ya kamata a cike shi bisa ƙa’idojin jam’iyyar.
Ya ce sashe na 15 da 16 na kundin tsarin mulkin Labour Party sun tanadi hanyoyin da ya kamata a bi wajen warware irin wannan matsala, don haka bai kamata wani mutum ya ɗauki matakin kafa shugabanci da kansa ba.
Mu’azu ya zargi Barde da gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar a Gombe tare da ayyana wasu mutane a matsayin shugabanni, ba tare da bin hanyoyin da jam’iyyar ta amince da su ba.
Ya jaddada cewa siyasar Barde da tsarin tafiyar Labour Party abubuwa ne mabambanta, yana mai cewa kasancewar mutum yana da tasiri ko goyon bayan wasu mambobi ba ya ba shi ikon mallakar jam’iyyar.
“Ba za a iya cewa tafiyar siyasar Mohammed Jibrin Barde ita ce Labour Party ba, kamar yadda Labour Party ba ita ce tafiyar Barde ba,” in ji Mu’azu.
Ya ƙara da cewa akwai mambobin jam’iyyar da dama a sassan jihar waɗanda ba sa cikin tafiyar Barde, amma suna da cikakken haƙƙin shiga harkokin jam’iyyar da neman muƙaman shugabanci.
A cewarsa, kwamitin zartarwa na jam’iyyar a jihar yana wakiltar dukkan mambobi, saboda haka halaccin shugabanci ya kamata ya dogara da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, ba ƙarfin wani mutum ko ƙungiyar siyasa ba.
Ɗan takarar gwamnan ya buƙaci Barde da ya dakatar da duk wani mataki na gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da guje wa ayyana wasu mutane a matsayin shugabanni har sai an bi ƙa’idojin da suka dace.
Ya ce duk wanda yake ganin yana da haƙƙin riƙe wani muƙami a jam’iyyar ya kamata ya gabatar da buƙatarsa ga hukumomin da abin ya shafa domin tantancewa da yanke hukunci bisa doka da tsarin jam’iyyar.
Mu’azu ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar na ƙasa da su fitar da matsaya a hukumance tare da sanar da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, domin kawo ƙarshen ruɗanin da ke tattare da shugabancin jam’iyyar a Gombe.
Ya bayyana cewa manufarsa ba ita ce rura wutar rikicin ba, sai dai tabbatar da adalci, kare martabar jam’iyyar da kuma bai wa kowane mamba damar shiga harkokin shugabanci ba tare da nuna bambanci ba.
Ya shawarci mambobi da magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, su guji musayar kalaman batanci tare da tabbatar da sahihancin bayanan da suke yaɗawa kan shugabancin jam’iyyar.
Mu’azu ya ce yana fatan matakin da shugabannin ƙasa za su ɗauka zai dawo da haɗin kai a jam’iyyar, domin mambobinta su mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen 2027.
Ƙoƙarin jin ta bakin Alhaji Mohammed Jibrin Barde domin samun martaninsa kan zarge-zargen bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
