Kotun wasanni ta tabbatar da Senegal a matsayin wadda ta lashe kofin AFCON na 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun kula da Shari’o’in Wasanni ta Afirka (CAS) ta mayar wa ƙasar Senegal matsayinta na wadda ta lashe kofin gasar Ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025, hukuncin da ya soke matakin Hukumar kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) na ƙwace nasarar tare da bai wa ƙasar Moroko.

An gudanar da shari’ar ne a ranar 24 ga Nuwamba, 2026, wadda aka yanke hukuncin aciki sakamakon ɗaukaka ƙara da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) ta yi, hukuncin da kuma ya dawo da nasarar ƙasar ta doke Moroko da ci 1 da nema a wasan ƙarshe na ranar 18 ga Junairun 2026.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen watanni ana rikicin shari’a akan wasan ƙarshen, wanda da fari ya bai wa Senegal nasara kafin kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya yi hukuncin bai wa Moroko nasara da ci 3 da 0.

Kotun wasannin ta tabbatar da ƙorafin da Senegal ta shigar a gabanta, matakin da ya sa ta soke hukuncin baya da ya bai wa Moroko nasara. Ita dai ƙasar Senegal tana ganin tunda har alƙalin wasa ya bari aka cigaba da wasan bayan bore da ‘yan wasanta suka yi ana tsaka da bugawa, to akwai buƙatar a tabbatar da sakamakon wasan yayin da aka kammala, wanda kuma shi ne CAS ta tsayu a kai.

By Babaji

Leave a Reply