Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Darakta Janar kuma babban mai tattaunawa na ofishin tattaunawar kasuwanci ta Najeriya (NOTN) kuma tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara, Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji, ya bayyana matuƙar alhini tare da miƙa ta’aziyya kan mummunan haɗarin mota da ya yi sanadiyar mutuwar magoya bayan jam’iyyar APC Mutum 15 a Jihar Zamfara.
Waɗanda suka rasu suna kan hanyarsu ne daga Gummi zuwa Talata Mafara domin halartar ƙaddamar da kamfen ɗin Gwamna na jam’iyyar a Talata Mafara a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da mummunan haɗarin ya faru.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Rikiji ya bayyana lamarin a matsayin babbar asara ba ga iyalan waɗanda suka rasu kaɗai ba, har ma ga ɗaukacin al’ummar Jihar Zamfara.
“Na samu labarin haɗarin da ya rutsa da magoya bayan jam’iyyarmu mai girma, APC, da matuƙar alhini da kaɗuwa. Allah ya jiƙansu da rahama kuma ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsu ta ƙarshe,” in ji Rikiji.
“Allah maɗaukakin sarki ya gafarta musu kurakuransu kuma ya ba iyalan su haƙuri da juriyar jure wannan babbar asara da ba za a iya maye gurbinta ba.”
Alh. Sanusi Rikiji, a madadinsa, iyalansa da ɗaukacin magoya bayansa na siyasa, ya miƙa ta’aziyya ga Gwamna Dauda Lawal, Sanata Abdul’aziz Yari (Darakta Janar, Kwamitin Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na APC), Alhaji Salihu Maibuhu Gummi (Darakta Janar, Kwamitin Kamfen ɗin Gwamna, da ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a Jihar ta Zamfara.
Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da daukacin al’ummar ƙaramar hukumar Gummi kan wannan rashi.
“Ina ƙara miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da ɗaukacin al’ummar ƙaramar hukumar Gummi kan wannan rashi,” ya ƙara da cewa.
Tsohon kakakin ya kuma roƙi Allah madaukakin sarki da ya sauƙaƙa wa waɗanda suka samu raunuka daban-daban a lokacin haɗarin, kuma Ya ba su saurin waraka gaba ɗaya.
Rikiji ya yi addu’ar Allah ya karɓi sadaukarwarsu, ya gafarta musu kurakuransu, kuma ya ba su Aljannatul Firdaus.
