Yadda Tinubu ya ceci takarar Buhari ta 2015 a kotu da rikicin da ya biyo baya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Da an soke sunan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga sahun ‘yan takarar shugaban ƙasa na 2015, ba dan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda a lokacin shi ne jagoran ƙasa na jam’iyyar APC, ya gaggauta tsoma baki wajen kiran Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Wole Olanipekun shiga tsakani a shari’ar kotu da ke barazana ga takararsa.

Tsohon ɗan jarida, Sam Omatseye ne ya bayyana haka a littafinsa mai suna From AD to APC: The Evolution of Nigerian Political Parties and the Eploits of One Man (1998-2015), a babi na 29, shafi na 483-485, wanda Shugaba Tinubu ya ƙaddamar a ranar Talata, a ɗakin taro na Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja. Littafin ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen fifita Buhari cikin ‘yan adawa da samar da shi a matsayin ɗan takarar da APC ta yi a 2015 da sadaukarwar siyasa da suka taimaka wa jam’iyyar karɓe mulki a lokacin.

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun kuma daɗaɗɗen ɗan jarida, Cif Aremu Segun Osoba, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa duk da gagarumar gudunmawar da Tinubu ya bayar wajen samar da APC da nasararta a zaɓe, gwamnatin marigayi Buhari ta yasar da shi bayan taimaka masa wajen samun nasara. Gwamnoni da wasu fitattun mutane da dama ne suka halarci taron gabatar da ababen da littafin ya ƙunsa ciki har da sadaukarwar Tinubu don tabbatar da Buhari ya cigaba da kasancewa cikin ‘yan takarar 2015.

A cewar bayanin da babin ya yi, kwanaki kaɗan kafin zaɓen na ranar 28 ga Maris, 2015 Tinubu ya kira Olanipekun a waya inda ya buƙaci da ya hanzarta tunkarar Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, yana mai gargaɗin cewa akwai yiwuwar a cire Buhari a cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa muddin ba a samu nasara ba a shari’ar kotun. Shugaba Tinubu a lokacin ya haƙura da dukkan wasu harkoki saboda muhimmancin al’amarin da ke fuskantar ɗan takarar APCn, inda ya sa ya tirje akan lallai sai lauyan ya bar Akure, Jihar Ondo ya je Abuja don warware matsalar.

Masu ƙarar a lokacin, sun tuhumi Buhari da ƙin miƙa takardun karatunsa ga Hukumar Zaɓe (INEC), matakin da suka ce ya saɓa wa Sashe na 131 da 318 na kundin dokar ƙasa na 1999 da Sashe na 31(3) na Dokar Ƙasa ta 2010. Wannan al’amari ya sa suka buƙaci kotu da ta haramta masa shiga zaɓen. Bayan shigar Olanipekun a matsayin mai kare waɗanda ake ƙara (Buhar da APC), Mai Shari’a Adeniyi Ademola, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranakun 22 da 23 ga Afrilu, domin bai wa Buhari damar zama cikin ‘yan takarar.

By Babaji

Leave a Reply