Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a KANO
Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai a jam’iyar PDP a ƙaramar hukumar Tarauni Hon. Abubakar Ibrahim Maina ya bayyana cewa a halin da ake ciki a ƙasar nan, ƙasar ba iya garanbawul ta ke buƙata ba face gina wata sabuwar Najeriya. Inda yace da zarar jam’iyar ta su ta dawo mulki a shekara mai zuwa za su sake fasalin gudanar ƙasar wanda al’umma za su dawo cikin hayyacin su.
Hon Abubakar Maina ya sanar da hakane a lokacin da ake ƙaddamar da sabbin shuwagabannin jam’iyar na mazaɓar Hotoron NNPC da ke ƙaramar hukumar Tarauni a ranar Lahadi da ta gabata. Ɗan takarar ya nuna godiyar sa da yadda al’ummar yankin su ke bawa takarar ta sa goyon baya da ma ita kanta jam’iyar ta PDP a yankin. Ya kuma musanta cewa jita jita da ake yaɗawa na cewa jam’iyar ta PDP ta mutu ba haka bane, jam’iyar tana nan kuma za ta sake kafa gwamnati a ƙasar shekara mai zuwa dan kuwa sheda ne lokacin tana mulki al’umma suna iya gudanar da komai cikin sauƙi saɓanin halin da ake ciki yanzu.
Ya kuma yi kira ga sabbin shuwagabannin da aka ƙaddamar da su mike tsaye wajen yaɗa manufofin jam’iyar da ta ‘yan takarkarunta musamman ma mata wajen shiga lungu da saƙo dan wayar da kan al’umma domin zaɓar jam’iyar PDP a ƙasar nan.
Itama a nata jawabin yayin taron, shugabar matan jam’iyar PDP reshen Arewa masu Yamma Hajiya Zainab Audu Baƙo cewa ta yi ba tayi mamakin yadda taga ɗimbin magoya baya ba da sauran al’umma sun halarci taron, domin har yanzu al’umma suna son jam’iyar, dan sun san yadda ta gudanar da irin na ta salon mulkin a ƙasar nan. Inda tace a halin da ake ciki al’umma sun nuna gajiyar su da salon mulkin da ake gudanarwa a wannan lokaci hakan yasa take da yaƙinin cewa ‘yan Najeriya za su sake zaɓar jam’iyar ta PDP dan sake dawowa ta mulki ƙasar a shekara mai zuwa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ƙaddamar da sabbin shuwagabannin, shugaban jam’iyar PDP na ƙaramar hukumar Tarauni kuma shugaban ƙungiyar shuwagabannin jam’iyar na ƙanana hukumomin jihar Kano Hon Sabiu Yusuf Muhammad cewa ya yi jam’iyar ta PDP itace uwa ga duk wata jam’iya a ƙasar nan domin a cewarsa itace ta haife ta.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su gujewa yin siyasar kuɗi, su rinƙa zaɓar yanci da cancanta don samun shugabanci nagari da samun sauyin halin da ƙasar ta samu kanta a ciki na tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.
A bayanin sa a madadin sauran waɗanda aka ƙaddamar shugaban jam’iyar na mazabar Hon Sunusi Akilu Suleiman ya nuna godiyar su bisa yadda aka zaɓo su don gudanar da sha’anin jam’iyar a yankin. Inda ya bada tabbacin cewa za su yi iya ƙoƙarin su wajen ganin jam’iyar ta samu nasara a zaɓe mai zuwa tare da duk yan takarkarunta.
Suma mazauna yankin sun bayyana cewa suna tare da yan takarkarun jam’iyar tun daga kan shugaban ƙasa zuwa kansila. Sun kuma yi roƙo ga yan takarar da cewa idan sun sami nasara su tuna da mazaɓar wajen sama mata abubuwa more rayuwa da magance musu wasu matsalolin da suka daɗe suna addabar su kamar rashin hanya, lalacewar ajujuwan makarantu yankin, ruwan sha da kuma harkar ilimin yaransu da tallafa wa mata da matasan yankin da jari don dogaro da kan su.
Taron ya samu halartar shuwagabannin jam’iyar na mazaɓun ƙaramar hukumar, shugaban jam’iyar na jihar Kano wanda jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyar ya wakilta, ɗan takarar sanata a Kano ta Tsakiya Hon Nafi’u Sankara, ɗan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano Hon. Injiniya Salisu Muhammad.
