Mazauna Ome a Nasarawa sun koka kan tsananin ƙarancin ruwa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Mazauna ƙauyen Ome da ke gundumar Duduguru a ƙaramar hukumar Obi a Jihar Nasarawa sun koka kan tsananin karancin ruwa, suna cewa yanzu tushen ruwan sh ɗaya da mutane tare da dabbobi.

Ƙauyen One a yankin wanda shine mafi girma a gundumar Duduguru kuma kewaye da wasu ƙananan ƙauyuka, ya cigaba da samun ƙaruwar jama’a cikin sauri saboda ayyukan noma da ke bunƙasa. Wannan ƙaruwar ta sa Ome ta zama mai muhimmanci a siyasance, musamman a lokacin zaɓe, amma mazauna sun ce wannan muhimmancin bai sauya zuwa ga abubuwan more rayuwa ba, musamman ruwan sha mai tsafta.

Da yake magana da wakilin mu da ya ziyarci fadar sa da ke Ome, Dagacin garin Ome mai suna Mista Luka Zhemuga, ya ce Ome ba ta da wani tushen ruwan sha mai aminci sai rijiyoyin burtsatse da mazauna da kansu suka haƙa.

Ya bayyana cewa mafi yawan rijiyoyin ba su da tsafta, ba su dace da sha ba, kuma suna bushewa ba da jimawa ba bayan damina ta kare, wanda hakan ke barin mazauna babu wani zaɓin sai yin tafiya mai nisa don neman ruwa.

Zhemuga ya koka cewa a lokacin rani, mazauna suna tilasta yin gasa da shanu da sauran dabbobi a kogi don ruwan sha, lamarin da ke fallasa su ga cutar kwalara, typhoid da sauran cututtukan da ke da alaka da ruwa, da kuma zazzaɓin cizon sauro.

“Idan muka shiga lokacin rani kamar haka, mutanena suna wahala da rashin ruwan sha, har wasu suna kamuwa da cutar kwalara, typhoid da sauran cututtuka masu alaƙa da ruwa,” in ji shi.

“Muna gasa da dabbobi a kogi don ruwan sha. Muna fama da zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka saboda ruwan ba shi da tsafta,” ya ƙara da cewa.

Dagacin ya ce matsalar ta daɗe shekaru da dama, duk da alƙawuran da ‘yan siyasa ke yi a lokacin yaƙin neman zaɓe na samar da ruwa ga al’ummar, alƙawuran da ya ce ba a taɓa cika su ba.

“Al’umma tana fuskantar ƙalubale da dama ta fuskar ruwa. Matanemu yawanci suna zuwa kogi; wasu suna zuwa da ƙarfe 4:00 na safe. Wannan matsalar ta dade da jimawa, kuma muna roƙon Allah gwamnati ta zo ta taimake mu,” in ji Zhemuga.

Da take magana itama wata mazauniyar garin, Misis Grace Abashi, ta ce mutanen Ome sun daɗe suna wahala da rashin ruwan sha mai tsafta a lokacin rani, tana mai lura da cewa mata suna fita daga gidajensu da karfe 5 na safe kuma suna shafe sa’o’i masu yawa suna jiran layi don samun ruwan sha daga kogin, wanda ke da nisan kilomita biyu daga al’ummar.

“Muna roƙon gwamnati ta taimake mu. Kada mu sake wahala da ruwa. Muna buƙatar rijiyar burtsatse; duk wani famfon ruwa da gwamnati za ta kawo mana, za mu yi farin ciki,” Abashi ta yi roko.

Haka kuma, shugaban matasa a al’ummar, Mista Elisha Akala, ya ce mazauna ba sa samun ruwa don amfanin gida, yana mai cewa lamarin ya ci gaba da haddasa matsalolin lafiya ga mutane.

Zhemuga, saboda haka, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Nasarawa da sauran hukumomin da abin ya shafa da su zo su taimaki al’ummar ta hanyar haƙa musu rijiyar burtsatse don kawo ƙarshen wahalar shekaru da dama da kuma kare su daga cututtukan da ke da alaƙa da ruwa.

By ukarofi

Leave a Reply