
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba tsararren tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya lashe amansa sakamakon janye iƙirarinsa na cewa shi da wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun naɗi hirar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu, inda ya tabbatar wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja cewa kalaman nasa ba gaskiya ba ne, saidai salon siyasa ne na ɗaukar hankalin jama’a da sanya gwamnatin cikin halin takura.
El-Rufa’i, wanda ya bayyana a matsayin mai kare ƙara na farko a gurfanarwar da Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta masa kan zarge-zargen cewa ya kutsa cikin hirar wayar tarho ta Ribaɗu da wasu tuhume-tuhume, ya ce da gangan ya yi iƙirarin don ya nuna cewa ‘yan ɓangaren adawa suna sanya ido kan waɗanda suke cikin gwamnati kamar yadda ita ma gwamnatin take sanya wa akan wasu.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana sane da cewa gwamnatin tana sanya ido akan jagororin adawa, tsofaffin shugabannin ƙasa, manyan alƙalai da wasu, saidai ya tirje akan cewa lallai shi da wasu ‘yan adawa ba su naɗi hirar Ribaɗu ba.
El-Rufa’i ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba a Abuja bayan lauyansa, Paul Erokoro (SAN), wanda ya jagoranci gabatar masa da hujjar da aka haska hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar 13 ga Fabarairun 2026, wadda a ciki ya yi iƙirarin naɗar hirar. El-Rufa’i ya ce ba yadda aka fahimci kalaman nasa yake nufi ba, amma hakan kalaman siyasa ne masu jan hankali waɗanda a cewarsa babu laifi a yi su acikin sadarwar siyasa.
Bayan sauraron bayanan da aka yi a zaman, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranakun 15 da 16 ga Fabarairu, 2027 domin bai wa El-Rufa’i damar cigaba da gabatar da masu ba shi kariya.
