Marubuciyar Arewa  ta lashe kyautar adabi a bikin Future Awards Africa na 2026

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Marubuciyar Najeriya, Fatima Bala, ta lashe kyautar adabi (Prize for Literature) a bikin bayar da kyaututtukan Future Awards Africa karo na 20, wanda aka gudanar a ranar 14 ga Nuwamba, 2026, a birnin Legas.

Bala, wadda aka haifa a Jihar Kaduna, ta samu nasarar ne tare sauran marubutan da aka zaɓa tare da ita, waɗanda suka haɗa da Damilare Kuku, Eloghosa Osunde da mawaƙi Peter Okonkwo.

Bikin na bana ya kasance na musamman kasanccewar sa karo na 20 da ake gudanar da kyaututtukan, waɗanda aka kafa domin karrama matasan Afirka masu ƙirƙira da kuma bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Fatima Bala marubuciya ce, mawaƙiya kuma malamar jami’a. Ayyukanta na rubuce-rubuce sun fi mayar da hankali kan soyayya, imani, zamantakewar iyali da kuma matsin lambar da al’umma ke ɗora wa mutane, musamman a cikin al’ummomin Arewacin Najeriya.

Daga cikin littattafan da ta rubuta akwai ‘Broken: Not a Halal Love Story’, Hafsatu Bebi da kuma The Lies We Tell, wanda tarin gajerun labaranta ne da ta wallafa a shekarar 2026.

Abin lura shi ne yadda marubuciyar ke amfani da labaran ƙagaggu wajen bayyana wasu batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum, musamman alaƙar da ke tsakanin addini, soyayya da zamantakewar al’umma.

Wannan nasara ta sanya Fatima Bala cikin jerin marubutan da suka taɓa lashe kyautar adabin Future Awards Africa, waɗanda suka haɗa da Ayọ̀bámi Adébáyọ̀, Akwaeke Emezi da Oyinkan Braithwaite.

Nasarar marubuciyar na ƙara fito da gudunmawar marubutan Najeriya wajen bunƙasa adabi, musamman a lokacin da ake samun sababbin marubuta da ke amfani da rubuce-rubuce wajen bayyana tunani, al’adu da ƙalubalen da al’ummominsu ke fuskanta.

By ukarofi

Leave a Reply