Sufeto-Janar ya dakatar da ayyana neman Shugaban THISDAY da wasu takwas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sufeto-Janar na Rundunar ‘Yan Sanda, Tunji Disu, ya sanar da dakatar da matakinsu na ayyana Shugaban gidan talabijin na Arise da jaridar THISDAY, Nduka Obaigbena da wasu mutane takwas a matsayin waɗanda ake nema bisa zargin su da hannu a zargin barazana ga rayuwar Darakta-Manaja na bankin FirstBank of Nigeria Limited.

Haka kuma, Disu ya umarci a miƙa binciken ga Reshen Binciken Leƙen Asiri na Rundunar (FID) a Abuja domin gudanar da bincike mai zurfi kuma ba tare da rinto ba. Rundunar ta sanar da haka ne awata takada da ta fitar a ranar Laraba ta hannun jami’in hulɗa da jama’arta, Anthony Iniedu.

Mataimakin Sufeto-Janar, Olohundare Jimoh ne ya ayyana mutane taran ne a matsayin waɗanda ake nema a ranar Talata, wanda shi ne jagoran ofishin Sashe na 2 yayin ganawa da ‘yan jarida a Legas. Waɗanda ake neman sune Ernest Azudialu-Obiejesi da Nnenna Azudialu-Obiejesi na Nestoil; Tope Shonubi na Sahara Group; Henry Kayode Ojogho na Broron Limited; Emmanuel Iheagwazi na Necit Nigeria Limited; Eze David na Energy Shield Petrochemical Limited; Emmanuel Orim da Victoria Orim na Luzen Plaza; da kuma Obaigbena.

A ranar Talata ne dai Jimoh ya sanar cewa binciken ya biyo bayan kai wani ƙunshin alburusan da aka samu na 7.62mm guda biyu a ciki zuwa gidan shugaban bankin a Legas. An ce wani ɗan aike ne ya kai ƙunshin da sunan kyautar kayan sakawa. Jagoran ‘yan sandan ya bayyana cewa bincike ya nuna yadda zargin barazanar ya samo asali daga ƙoƙarin da FirstBank ke yi wajen dawo da biliyoyin kuɗaɗen rance da ake bin kwastomomin FirstBank.

A cewar Jimoh, an gayyaci kwastomomin banki guda 10 da wasu domin binciken a ranar 5 ga Nuwamba kuma aka umarci su amsa a ranar 12 ga Nuwamba. Saidai mutum guda ne kaɗai ya amsa gayyatar, lamarin da ya sa hukumar ta ayyana sauran a matsayin waɗanda ake nema ruwa-a-jallo, ciki har da shugaban na THISDAY. A yanzu dai, rundunar ‘yan sandan ta mayar da binciken hannun FID, inda aka buƙaci baki ɗaya waɗanda aka alaƙanta da al’amarin su je Abuja yayin da hukumomi suke ƙoƙarin gano haƙiƙanin al’amari game da zargin.

Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Obaigbena ya caccaki rundunar akan matakin ayyana shi a matsayin wanda ake nema, inda a wata sanarwa ya ce bai samu wata takardar gayyata da ta shafi binciken daga ‘yan sanda ko wata hukuma a kowane gurarensa ba duk da cewa a ‘yan makonnin nan yana tattaunawa da manyan jami’an ‘yan sanda har a ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba akan kafa ‘yan sandan jihohi, kuma babu wata alama da ke nuna cewa ‘yan sanda na son ganin sa akan wani bincike.

By Babaji

Leave a Reply