Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Mambobin reshen Kwankwasiyya Amana na Zamfara sun bayyana goyon bayansu a hukumance ga Sanata Kabir Garba Marafa a matsayin ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaɓe mai zuwa.
Ƙungiyar ta kuma shiga wata ƙawance da Marafa Ambassadors for Change domin samun nasara ga Sanata Marafa a matsayin gwamna a ƙarƙashin NDC.
An bayyana haɗin gwiwar ne a ƙarshen wani taro tsakanin shugabannin Kwankwasiyya Amana Zamfara da ƙungiyar Marafa Ambassadors for Change a Gusau yau Alhamis.
Shugaban Kwankwasiyya Amana, Usman Muhammad Sani Maru, ya ce mambobin tawagar sun haɗa da wakilai daga dukkan mazaɓu 147 da ke faɗin Jihar Zamfara, da dukkan masu gudanarwa na ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin goyon baya daban-daban, da shugabannin mata.
Ya ƙara da cewa, dukkan ‘yan takarar da suka fafata a zaɓen da ya gabata a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP suma sun halarci zaman domin bayyana goyon bayansu ga Sanata Kabir Garba Marafa.
Ya ce reshen Kwankwasiyya Amana na Zamfara ya amince ya zama mamba a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a jihar.
A cewar ƙungiyar, nasarar Sanata Kabir Garba Marafa da ci gaban Jihar Zamfara a ƙarƙashin NDC ne babban abin da suka sa a gaba.
Ƙungiyar Kwankwasiyyar ta tabbatar wa Sanatan goyon bayanta, inda ta yi alƙawarin tsayawa tare da shi don samun nasarar sa a zaɓen da ke tafe.
Sun yi alƙawarin gudanar da wani gagarumin yaƙin neman zaɓe na gida-gida, inda za su yi aiki dare da rana domin wayar da kan masu zaɓe da kuma tabbatar da nasara ga Sanata Marafa a zaɓe mai zuwa.
Ƙungiyar ta amince da Commander Modibbo Aminu Marafa, wanda ya kafa Marafa Ambassadors for Change, a matsayin shugabanta, inda ta bayyana cewa ya mu’amalance su da girmamawa, mutunci, da kyakkyawar niyya.
Ƙungiyar Kwankwasiyyar ta bayyana Sanata Marafa a matsayin shugaba mai kirki, mai karamci, kuma mai gaskiya, wanda ba za a iya yaudara, ko a ci amanarsa ba, kuma wanda ba ya watsar da magoya bayansa bayan ya yi amfani da su.
Ƙungiyar ta bayyana gwamnatin da ke mulki a yanzu a Jihar Zamfara a matsayin wacce ta gaza matuƙa, inda ta bayyana cewa hakan ya sa ya zama wajibi Sanata Marafa ya karɓi mulki don kawo ci gaba da wadata.
A martaninsa, Auwal Abdullahi Dalla Dalla, babban mamba a Marafa Ambassadors for Change, yayi maraba da sabuwar ƙawancen da reshen Kwankwasiyya Amana na Jihar Zamfara ya yi.
Ya tabbatar musu cewa za su yi aiki tare da su cikin haɗin kai, da girmamawa domin nasarar takarar Sanata Kabir Garba Marafa a matsayin Gwamna.
Ya yi alƙawarin haɗin gwiwa mai albarka da aka gina bisa girmamawa da manufofi ɗaya, yana mai jaddada cewa ƙarfin haɗakarsu ne zai zama ginshiƙin nasarar wannan tafiya.
