Wallafar: ABDULHAMID M. SANI MATAZU
“Marubuta ya ya haƙurin marubuciya Jamila Allah ya gafarta wa Jamila Umar Tanko”
1. Bismillah Tabarakka,
Zan tsara yau baituka,
Wurin ɗayar baiwarka,
Da kak kira ta gare ka,
Hajiya Jamilatu Tanko.
2. Salati farkon fari,
Ga Sayyadul-Bashari,
Mai son sa na kan khairi,
Alai Sahab ba ni bari,
Kan baitukan in aiko.
3. Baƙin cikinmu mutane,
Dukkanmu nan mamata ne,
Zamanmu nan na gwaji ne,
Yau ga shi mun daɗa gane,
Mun rasa ‘ya gun Tanko.
4. ‘Ya’ya da ‘yan’uwanki,
Gami da mai ɗakinki,
Sun fi mu ji na rashinki,
Allah ya rahamshe ki,
Jamila Umar Tanko.
5. A madadin marubuta,
Ta’aziyya mun miƙata,
Dukkanmu maza mata,
Allah yasa ki na’imta,
Aljanna mai fifiko.
6. Duk madadin ikhwana,
Mu marubuta juna,
Malumma addu’ana,
Allah yasa ki a Jannah,
Firdausi mai fifiko.
7. Domin Habibi Nura,
Annabi Baban Zahra,
Ruwa na Alkausara,
Allah ya ba ki ya ƙara,
Jamila Ummaru Tanko.
8. Abdulhamidi ya yi ta,
Na-Matazu ni na rubuta,
Babansu Fatima Binta,
Nai don mu rinƙa tuna ta,
Allah ka bamu iko.
Alhamdulillah !!!
