Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihohin Kano, Delta, Ribas, Edo, Ondo da Kebbi sun kasance kan gaba wajen fuskantar tashe-tashen hankula da suka shafi siyasa gabanin babban zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027, a cewar wani sabon rahoto da ƙungiyar Ci Gaban Kimpact (KDI) ta fitar.
Rahoton, wanda aka ƙaddamar a ranar Laraba a Abuja, ya bayyana cewa jihohin shida sun fi samun munanan rikice-rikice cikin jimillar hare-hare 124 da aka rubuta a jihohi 35 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja, tsakanin 1 ga Yuli zuwa 23 ga Nuwamba, 2026. Rikice-rikicen sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 22.
Jihar Delta ce ta fi yawan asarar rayuka, inda mutum biyar suka mutu sakamakon hare-hare 10. Sai Jihar Kano, wadda mutum uku suka rasa rayukansu cikin hare-hare 11, yayin da a Jihar Ribas mutum ɗaya ya mutu cikin hare-hare 10. Haka kuma, rahoton ya sanya jihohin Edo, Ondo da Kebbi cikin jihohin da suka fuskanci munanan tashe-tashen hankula. Wannan na nuna cewa matsalar ta bazu a sassa daban-daban na ƙasar, maimakon kasancewa a wasu yankuna kaɗan kamar yadda aka saba gani.
An tattara bayanan waɗannan rikice-rikice ne ta hanyar wani shiri na KDI mai suna Nigeria Election Violence Education and Reporting (NEVER), wanda ke bibiyar tashe-tashen hankula da suka shafi zaɓe, tare da wayar da kan jama’a da bayar da rahotonsu. ƙungiyar KDI, wadda ba ta neman riba, ba ta goyon bayan wata jam’iyya kuma ba ta ƙarƙashin gwamnati, ta ce yanayin siyasa gabanin zaɓen na ƙara fuskantar barazanar tsoratarwa, farmakin jiki, garkuwa da mutane, harbe-harbe, lalata kayayyakin kamfen da sauran nau’o’in tashe-tashen hankula da suka samo asali daga siyasa.
Rahoton ya nuna cewa rikice-rikicen sun ƙaru matuƙa yayin da ranar zaɓe ke ƙaratowa. A watan Yuli an samu hare-hare uku kacal, amma adadin ya haura zuwa 48 a watan Oktoba, sannan aka sake samun wasu hare-hare 40 a rabin farkon watan Nuwamba. KDI ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar lamarin ya ƙara ta’azzara a jihohin shida da ma sauran sassan ƙsar, idan jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka gaza ɗaukar matakan gaggawa.
ƙungiyar ta danganta ƙarin rikice-rikicen da ƙaruwar rashin haƙuri tsakanin ’yan siyasa da kuma kalaman tunzura jama’a da wasu jagororin siyasa da magoya bayansu ke yi. Sai dai ta jaddada cewa matsalar ta shafi jam’iyyun siyasa daban-daban, don haka bai kamata a ɗora alhakin ta kan wata jam’iyya ko ƙungiya guda ba.
Ta buƙaci ’yan takara, masu magana da yawun jam’iyyu da ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓe da su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar al’umma, manufofi da shirye-shiryen da suke da su, maimakon amfani da kalaman da za su iya tayar da ƙiyayya ko haddasa rikici.
A yayin da take bayyana yadda rikice-rikicen suka kasu a faɗin ƙasar, KDI ta ce: Farmakin jiki ya kai kashi 46.8 cikin 100, Lalata dukiyoyi ya kai kashi 28.8 cikin 100, Harbe-harbe ya kai kashi 10.2 cikin 100, Tsoratarwa da cin zarafi sun kai kashi 9 cikin 100, Garkuwa da mutane ya kai kashi 4 cikin 100.
ƙungiyar ta ce magoya bayan jam’iyyun siyasa, ma’aikatan gwamnati, ’yan jarida da sauran ’yan ƙasa na ƙara fuskantar barazanar tsoratarwa saboda amfani da haƙƙoƙinsu na dimokuraɗiyya. Saboda haka, ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da ’yan takara, musamman waɗanda ke fafatawa a jihohin shida da rahoton ya ambata, da su fito fili su yi alƙawarin gudanar da kamfen cikin lumana, tare da hana magoya bayansu shiga duk wani nau’in tashin hankali.
Haka kuma, ta buƙaci hukumomin tsaro da su ƙara tura jami’ai zuwa wuraren da aka gano akwai barazanar rikici, tare da gaggauta ɗaukar mataki idan aka samu alamun tashin hankali. Ta kuma jaddada cewa ya kamata a tabbatar da aiwatar da dokokin zaɓe ba tare da nuna son kai ba. KDI ta kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan masu zaɓe da kuma ƙoƙarin shawo kan rikice-rikice, musamman a Kano, Delta, Ribas, Edo, Ondo da Kebbi.
Bugu da ƙari, ta buƙaci wungiyoyin farar hula, cibiyoyin addini, sarakunan gargajiya da kafafen yaɗa labarai da su taka rawar gani wajen bunƙasa haƙuri da juna da kuma siyasa bisa mutunta juna. Ta kuma yi kira ga ’yan ƙasa da su ƙi amincewa da tashin hankali, tare da kai rahoton duk wata barazana ga hukumomin da abin ya shafa ta hanyoyin da suka dace.
ƙungiyar ta jaddada cewa ya kamata kowane ɗan Nijeriya ya samu damar shiga harkokin zaɓe ba tare da fargabar tsoratarwa, tilastawa ko ramuwar gayya ba. Ta kuma yi gargaɗin cewa sakamakon zaɓe ya kamata ya kasance abin da ya nuna zaɓin ’yan ƙasa, ba sakamakon barazana ko amfani da ƙarfi ba.
