Hare-haren ’yan ta’adda sun ragu da kashi 75 cikin 100 – Fadar Shugaban ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya ce hare-haren ’yan ta’adda a Nijeriya sun ragu da kashi 70 zuwa 75 cikin 100 a cikin watanni uku da suka gabata.

Dare ya danganta raguwar hare-haren da ƙara zafafa ayyukan yaƙi da ta’addanci da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na APC ya gudanar a Legas.

Ya ce bayanan rundunar soji sun nuna an samu gagarumin ci gaba, ciki har da cafke shugabannin ’yan ta’adda da kuma dakile hare-hare.

Dare ya kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙara yawan rundunonin sojin ƙasa daga takwas zuwa 12 domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro.

Ya ce gwamnati na shirin ɗaukar sababbin jami’an ’yan sanda 50,000 da sojoji 24,000, tare da horar da jami’an tsaron dazuzzuka domin yaƙi da ’yan bindiga.

A cewarsa, jihohi 16 ne suka zuwa yanzu suka cika sharuddan ɗaukar jami’an tsaron dazuzzuka, inda ake sa ran kowace jiha za ta ɗauki jami’ai 1,000.

Mai ba shugaban ƙasar shawarar ya kuma bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi na daga cikin muhimman matakan da za su taimaka wajen inganta tsaro, saboda hakan zai kusantar da jami’an tsaro ga al’umma.

Ya ce ana tattaunawa kan kafa ’yan sandan jihohi kusan shekara 21, kuma tsarin gyaran kundin tsarin mulkin da zai ba da damar hakan ya kai matakin jiran matakin shugaban ƙasa.

Dare ya jaddada cewa shawo kan matsalar tsaro na buƙatar ci gaba da zuba jari, sauye-sauyen hukumomi da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi, yana mai cewa ba za a iya kawo ƙarshen matsalar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba.

By ukarofi

Leave a Reply