Dalibai 153 ne suka sauke Alƙur’ani a makarantar Sheikh Umar

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kimani dalibai 153, maza da mata, sun yi nasarar haddace Littafin Alƙur’ani Mai Girma a Kwalejin Koyar da Alƙur’ani ta Sheikh Umar da ke Dawakin Kudu, a ranar Asabar da ta gabata. An gudanar da taron saukar a filin makarantar.

Da yake jawabi yayin taron, Daraktan makarantar, Malam Lawan Tijjani Umar, ya bayyana godiyarsu ga Allah da Ya nuna musu wannan rana mai albarka. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yadda makarantar ke samun ƙarin masu saukar Alƙur’ani a duk shekara.

Ya ce a baya ana samun mata masu saukar Alƙur’ani fiye da maza, amma a wannan shekara adadin maza ya ƙaru, ya kai kusan na mata. Ya ce abin da ke sa mata su fi maza yawa a wasu makarantun Islamiyya shi ne yadda mata suka fi yawa a cikin al’umma, tare da juriya da suke nunawa wajen karatu.

A cewarsa, wasu lokuta maza kan fara karatu amma su daina zuwa sakamakon dawainiyar rayuwar yau da kullum.

Ya ja hankalin ɗaliban da su yi amfani da ilimin da suka koya da kuma abin da Alƙur’ani ya koyar. Ya kuma yaba wa iyaye da malaman makarantar bisa yadda suka ɗauki nauyin yaran har zuwa wannan rana da suka sauke.

Shi ma shugaban makarantar, Malam Hamisu Sani Muhammad, baya ga taya ɗaliban murnar saukar da suka yi, ya kira gare su da cewa karatu bai tsaya ga saukar Alƙur’ani kawai ba, har ma da rubuta shi, haddace shi da kuma aiki da abin da ya koyar.

Ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ’ya’yansu sun ci gaba da karatu, har da na zamani. A cewarsa, a yanzu ana koyon Alƙur’ani da kuma koyar da shi ta hanyoyin zamani.

Kazalika, shugaban makarantar ya jinjinawa iyaye bisa dagewarsu wajen ganin yaran sun samu damar haddace Alƙur’ani. Ya kuma gode wa waɗanda suka halarci taron saukar da makarantar ta saba shiryawa duk shekara.

Wasu daga cikin ɗaliban da muka zanta da su jim kaɗan bayan kammala saukar, Maryam Muhammad Ibunu Alhassan da Atiku Hussaini Salisu Sheshe, sun bayyana farin cikinsu da ganin wannan rana da suka sauke Alƙur’ani. Sun ce wannan wata dama ce da suka samu ta ci gaba da neman ilimi.

Sun kuma gode wa iyayensu da malamansu bisa juriya da ɗaukar nauyin karatunsu tun daga farko har zuwa wannan lokaci.

By ukarofi

Leave a Reply