Kwamishinan gona a Kano ya raba tallafin miliyan N10

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU, a Kano

Kwamishinan Gona na Jihar Kano, Dakta Danjuma Mahmud Yamkatsari, ya raba tallafin kuɗi naira miliyan 10 ga mutum 125 a mazabarsa, inda kowannensu ya samu naira dubu 80 domin inganta sana’arsu da dogaro da kai.

Kwamishinan, wanda Mataimakinsa na Musamman, Alhaji Ibrahim Bala Yamkatsari, ya wakilta tare da wasu jagororin jam’iyyar APC a mazabar, ya ce wannan tsari ne na kwamishinan na taimaka wa al’umma domin bunƙasa sana’o’insu da dogaro da kai.

Ya ce burinsa shi ne taimaka wa al’ummar da ba su samu damar yin karatu ba, domin su ma su zama masu amfani a cikin al’umma. Ya ƙara da cewa a baya kwamishinan ya samar wa matasa da dama aikin gwamnati a matakai daban-daban domin su ma su dogara da kansu.

Haka kuma, ya ce a baya mata sama da dubu uku ne suka amfana da tallafin kuɗi naira dubu 50 kowaccensu a mazabu 30 da ke ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa. Tallafin ya fito ne daga kwamishinan noma da gudanar da sana’o’i, domin taimaka wa matan su dogara da kansu.

Ya ja hankalin waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin yadda ya dace, domin a nan gaba su ma su taimaka wa wasu. Ya kuma kira gare su da su ci gaba da yi wa gwamnati addu’a da ba ta goyon baya a zaɓe mai zuwa. Ya ce idan gwamnati ta samu nasara, abin da za su gani zai fi haka.

Wani jagora da muka zanta da shi ya nuna godiyarsa ga kwamishinan bisa wannan ƙoƙari da yake yi wajen tallafa wa al’umma, ba kawai a mazabarsa ko ƙaramar hukumarsa ba, har ma da wasu maƙwabtansu. Ya kuma yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin da aka ba su wajen gina kansu da kuma taimaka wa waɗanda suka dogara da su.

A nasu ɓangaren, waɗanda suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu, tare da gode wa kwamishinan bisa tallafin da ya ba su. Sun tabbatar da cewa za su yi amfani da kuɗin yadda ya dace.

By ukarofi

Leave a Reply