A ƙarshe, an tabbatar da rusuwar Raiola, wakilin Pobga da Ibrahimovic

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗaya daga cikin fitattun wakilai kuma fitattu a fagen wasan ƙwallon ƙafa a duniya, Mino Raiola, ya mutu yana da shekara 54, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

Raiola ya wakilci wasu manyan mutane a ƙwallon ƙafa da suka haɗa da Paul Pogba da Erling Haaland da kuma Zlatan Ibrahimovic.

Ya yi aiki a fagen ƙwallon ƙafa tun a shekarun 1980 kuma ya kasance tsayayye a wasu manyan yarjejeniyoyin da aka ƙulla a duniyar ƙwallon ƙafa, irinsu fam miliyan 89 da Pogba ya yi a duniyar a lokacin da ya koma Manchester United a 2016.

Wata sanarwa daga iyalansa da aka buga a shafukan sada zumunta ta ce, “a cikin baƙin ciki mara musaltuwa, muna bayyana rasuwar wakilin ƙwallon ƙafa mai suna Mino Raiola.