A karon farko an yi tozali da abokin karatun Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Durojaiye Ogunsanya, ya bayyana shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin abokin karatunsa a Jami’ar Jihar Chicago da ke Ƙasar Amurka (CSU).

A yayin da ya ke magana a wani shiri na TVC, Ogunsanya ya ce shi da shugaban Nijeriya sun kammala karatun digiri a sashin kula da harkokin kuɗi da kasuwanci a shekarar 1979.

Idan za a iya tunawa, taƙaddama kan karatun shugaba Tinubu ya kasance abin cece-kuce kamar yadda wasu abokan hamayyarsa na siyasa suka ce Tinubu bai  halarci jami’ar CSU ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, yana ɗaya daga cikin masu ƙalubalantar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa a 2023, inda ya shigar da ƙara a wata kotu a Amurka, yana neman jami’ar CSU ta samar da tarihin karatun Tinubu.

Amma da yake magana kan shirin, Ogunsanya ya ce ya san shugaban a makaranta.

“Mun haɗu a wata makaranta a jihar Chicago; muna sashen da ake kira ‘College of Accounting, Business and Administration’, muna a fannin lissafi, kuma muna aji ɗaya tare muka kammala. Ya halarci jami’a kuma ya kammala a 1979 kamar yadda na yi. Don haka na zo nan ne don in shaida cewa ya halarci Jami’ar, kuma ɗalibi ne na ƙwarai.”

Da aka tambaye shi ko mene ne ra’ayinsa lokacin da mutane suka ce Tinubu bai kammala karatunsa ba, Ogunsanya ya ce, “Mutane su na tafka kuskure. Domin mutumin ya yi gwamna shekara 8, kuma ya yi aiki a Mobil shekaru da yawa, sannan a ce bai je jami’a ba, shin hakan zai yiwu? Ba zan iya tunanin yadda hakan zai yiwu ba.”