Yadda babban layin lantarki ya jefa Nijeriya duhu

*Minista ya yi ƙarin haske
*Wannan ne duhun-duhununa na farko a mulkin Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Wutar Lantarki na Tarayyar Nijeriya, Adebayo Adelabu ya ce an samu fashewar wani abu da ya kai ga ɓarkewar gobara a tashar wuta ta Kainji/Jebba da ke yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya.

Adelabu a cikin jerin saƙon a dandalin sadarwa na X a jiya Alhamis ya ce, da ƙarfe 04:35 na asubahin Alhamis an ji tashin gobara tare da ƙarar fashewar abubuwa a layin Kainji/Jebba mai qarfin 330KV Line 2 (Cct K2J) Blue Phase CVT da Blue Phase Line Isolator na Kainji/Jebba 330KV Line1, inda aka ga yana ƙonewa.

“Wannan ya haifar da raguwa sosai a mita daga 50.29Hz zuwa 49.67 Hz a 0:35:06Hrs tare da asarar ƙarni na Jebba na 356.63MW.”

Ya kuma ba da tabbacin cewa, za a gyara matsalar, yana mai cewa, “muna kan lamarin kuma ana cigaba da maido da aiki cikin gaggawa.

“An kashe gobarar kuma sama da rabin abubuwan haɗin sun tashi kuma sauran za a dawo da su gabaɗaya. Godiyata ƙwarai da gaske ga waɗanda suka amsa ko suka nuna damuwa ta hanyoyi daban-daban.”

Blueprint Manhaja a baya ta ruwaito cewa, wutar lantarkin ƙasar ta ragu da kashi 93.5 zuwa megawatts 273 a safiyar Alhamis.

Bayanan da Manhaja ta samu daga Hukumar Nigeria Electricity System Operator da ke hannun mai cin gashin kansa na Kamfanin Transmission Company of Nigeria, TCN, ya nuna cewa, tashoshin Afam VI, Daɗinkowa, Ibom Power, Jebba da Olorunsogo sun samar da 0.70MW, 0.00MW, 32.90MW, 240MW da sifili. bi da bi.

Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos, a ranar Alhamis sun nemi afuwar masu amfani da hasken lantarki a ƙasar, inda suka yi alƙawarin dawo da wadatar wutar lantarki idan al’amura suka daidaita.

Haka zalika, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja, AEDC, ya bayyana cewa: “Hukumomin AEDC na son sanar da abokan hulɗarsu cewa matsalar wutar lantarkin da ake fuskanta a halin yanzu ta samo asali ne sakamakon gazawar tsarin da na’urar sadarwa ta ƙasa ta yi a safiyar Alhamis, 14 ga Satumba, 2023.

Wata sanarwar da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Enugu (EEDC) ya fitar, ta ce durƙushewar ta afku ne da misalin ƙarfe 12:40 na safe wanda ya yi sanadin ɗaukewar wuta a faɗin ƙasar.

“Saboda wannan lamarin na durƙushewar layin wutar lantarki a Nijeriya, duk tashoshinmu na TCN ba su da wadatar tura wuta wanda hakan ya sa ba za mu iya tura wuta ga abokan cinikinmu a jihohin Abiya da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo ba.”

Wannan dai shi ne karon farko da aka fuskanci matsalar durƙushwar babban layin wuta na ƙasa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *