A karon farko kuɗin ajiyar Nijeriya a waje ya kai Dala 40.08bn tun 2022

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani rahoto da babban bankin Nijeriya, CBN ya fitar, ya ce kuɗin ajiyar ƙasar da ke waje ya ƙaru inda ya kai Dala biliyan 40.08 a ranar 7 ga watan Nuwamba wanda wannan shi ne mafi yawa da aka samu a kusan shekaru biyu.

Hakan ya taimaka wajen samun gagarumar nasara da tsare-tsaren CBN suka taimaka aka cimma na bunƙasa hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje bisa hanyoyin da doka ta amince da su.

A watan Satumba ne adadin kuɗaɗen ajiyar ya kai Dala biliyan 38.3 inda aka samu hauhawarsa har zuwa matakin da ya kai a yanzu.

Kasuwannin duniya da na harkokin mai sun taimaka wajen haɓaka kuɗaɗen ajiyar.

CBN ya duƙufa ne wajen cuɗanya da masu aikin jujjuya kuɗin a mataki na ƙasa-da-ƙasa wanda zai dace da tsarin da Nijeriya ke a kai ta fuskar inganta harkokin ƙuɗaɗe.

A yayin wani taron ƙara wa juna sanine a Abuja, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana yadda cinikayyar manyan kasuwannin duniya suka yi tasiri wajen hauhawar kuɗaɗen.

Ya kuma jaddada cewa, CBN na ƙoƙari wajen ganin an cimma nasarar da ta haura abin da aka samu a yanzu ta hanyar yin aiki tuƙuru da masu-ruwa-da-tsaki da kuma tsare-tsare da za su taimaka wa hakan.

By Babaji