Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen bunƙasa ɓangaren kasuwancin Nijeriya yana haifar da sakamako mai kyau, inda Nijeriya ta samu ribar kasuwanci mai darajar naira tiriliyan 6.5 a zangon ƙarshe na shekarar 2024. Shettima, wanda aka wakilta ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya bayyana haka a taron ƙasa na uku kan fitar da kayan da ba su da alaƙa da man fetur, da aka shirya a ranar Talata a Abuja. Wannan taro, wanda hukumar bunƙasa fitar da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC) ta shirya, ya samu taken “Bunƙasa Fitar Da Kayayyakin Da Ba Su Da Alaƙa Da Man Fetur Don Ingantaccen Tattalin Arzikin Ƙasa.”
A cewar Shettima, sabuwar manufar kasuwancin da aka aiwatar kwanan nan tana da nufin ƙarfafa ɓangaren kasuwanci don ya ƙara taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziki, tare da haɓaka matsayinsa a kasuwancin duniya. “Domin Nijeriya ta samu cigaba a fannin ribar kasuwanci, akwai buƙatar tabbatar da ingantaccen aiwatar da wannan sabuwar manufa ta kasuwanci,” in ji shi. Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana cewa, an samu ribar kasuwanci mai darajar naira tiriliyan 6.5 a zango na biyu na shekarar 2024, inda fitar da kayayyaki ya kai kashi 60.89 na jimillar kasuwancin naira tiriliyan 19.42.
Ya kuma ƙara da cewa, wannan nasarar ta nuna ƙaruwar kaso 1.31 daga zangon farko na shekarar, da kuma ƙaruwar kaso 201.76 daga zango na biyu na shekarar 2023. Shettima ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na rage dogaro da man fetur ta hanyar bunƙasa ɓangarorin da ba su da alaƙa da man. Haka zalika, ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki matakin rage tsauraran dokokin kasuwanci domin sauƙaƙa wa ƙanana da matsakaitan masana’antu damar yin kasuwanci cikin sauƙi.
A yayin da yake jaddada muhimmancin cin gajiyar damar da yarjejeniyar kasuwanci ta Afirka (AfCFTA) ke bayarwa, Shettima ya gargaɗi Nijeriya da kada ta zama wurin zubar da kayan ƙasashen waje. Shugabar NEPC, Mrs Nonye Ayeni, ta danganta ƙaruwar kuɗin shiga daga kayayyakin da ba su da alaƙa da man fetur da dabarun manufofin Shugaba Bola Tinubu. Ayeni ta bayyana cewa, kuɗin shiga daga fitar da kayayyaki da ba su da alaƙa da man fetur sun ƙaru da kaso 6.26 a farkon rabin shekarar 2024, inda ya kai dala biliyan 2.7.
Ta ƙara da cewa, shirin “Operation Double Your Export” na NEPC, wanda ke da nufin bunƙasa fitar da kayayyaki daga Nijeriya ta hanyar tallafawa ɓangarorin noma, ma’adinai, da kayayyakin masana’antu, yana taka muhimmiyar rawa. Haka zalika, ta bayyana cewa NEPC ta ɓullo da shirye-shirye da suka haɗa da ba da takardar izini ga ‘yan kasuwa, samar da ɗakin ajiya na ƙasa domin sauƙaƙa harkar jigila da kuma rage yawan kayayyakin da ake mayarwa daga ƙasashen waje. Wannan taron ya tara shugabannin masana’antu, ‘yan kasuwa, da masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci don tattaunawa kan ƙalubale da damar da ke akwai wajen faɗaɗa kasuwancin da ba shi da alaƙa da man fetur tare da samun hanyoyin faɗaɗa tattalin arzikin Nijeriya.
