A karon farko PSG ta lashe Super Cup bayan doke Tottenham a bugun fenareti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Paris Saint Germain ta doke Tottenham Hotspur da ci 4 da 3 a bugun ‘daga kai sai mai tsaron gida’, lamarin da ya ba ta damar lashe Kofin UEFA Super Cup a karo na farko a tarihinta.

An tashi wasan ne 2 da 2 bayan da PSG ta farke ƙwallo biyu da Tottenham ta fara zura mata ana ƙasa da mintuna 15 da ƙarƙare wasan.

Da fari Spurs ce ta samu damar nasara a wasan, ƙarƙashin sabon kocinta, Thomas Frank, yayin da ta jagoranci wasan da ci 2 da nema jim-kaɗan da koma wa hutun rabin lokaci ta hannun ƴan wasa Micky Van de Ven da Cristian Romero.

PSG ta farfaɗo ne a lokacin da Lee Kang-in ya farke ɗaya a minti na 85 yayin da Goncalo Ramos ya zura ta biyun bayan minti huɗu na ƙarin lokaci.

Wannan shi ne karo na farko da wata ƙungiya daga ƙasar Faransa ta lashe Super Cup, lamarin da kuma ya kai adadin kofunan da PSG ta lashe a 2025 zuwa biyar.

By Babaji