Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar Ƙaura Namoda bisa hare-haren ‘yan bindiga

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya ziyarci ƙauyukan Banga, Sakajiki da Kuryar Madaro da wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda da ke jihar.

An kashe mutanen yankin da dama tare da jikkata wasu da dama inda maharan suka yi garkuwa da wasu yayin harin makonnin da suka gabata.

Gwamnan wanda ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi da ta haɗa da mataimakin sa Mani Mumuni da sakataren gwamnatin jihar Abubakar Nakwada da sauran manyan jami’an gwamnati sun ziyarci al’ummomin ne a yau Laraba domin jajanta wa jama’a kan abin da ya kira ƴan ta’addan a matsayin maƙiya zaman lafiya.

Gwamnan ya umurce al’ummomin da su ɗauki lamarin a matsayin ƙaddara daga Allah tare da ba su tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin magance matsalar rashin tsaro.

Gwamna Lawal yace, gwamnatin sa za ta cigaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.

“Mun zo nan ne domin jajanta muku kan harin da ‘yan bindiga suka kai muku, addu’a ita ce Allah ya jiƙan waɗanda suke rasa rayukansu baki ɗaya, ya kuma warkar da waɗanda suka jikkata, ya kuma bai wa waɗanda akayi garkuwa dasu mafita.”

“A matsayinmu na gwamnati, muna yin iya ƙoƙarin mu don ganin cewa ‘yan bindiga sun zama tarihi a jihar kuma fa yardar Allah haka za ta tabbata.”

” Ina roƙon Allah ya tona asirin masu kashe-kashe da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a jiharmu, waɗanda kuma suke farin ciki idan ana kashe mutane saboda son ransu a siyasance su ma ba za su gama lafiya ba da yardar Allah”.

Gwamnan ya kuma buƙaci jama’a da su ƙara zage damtse domin ganin an dawo da zaman lafiya a duk wuraren da ake fama da rikici.

“Ina kira gare ku da ku yi addu’a domin gaggauta kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda, da masu ɗaukar nauyin su, masu haɗa kai dasu ” Gwamna Lawal ya ƙara da cewa.

Gwamnan yayi addu’a cewar Allah ya tona asirin duk masu hannu a harkar ta’addanci a jihar da masu siyasantar da harkar tsaro.

Gwamna Lawal ya ƙara da cewa “Dole ne mu ci gaba da bin kadin wannan mummunan aiki na kisa da garkuwa da mutane.”

Sarakunan gargajiya da wasu daga cikin al’ummar yankin da abin ya shafa sun gode wa gwamnan bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai masu tare da tabbatar masa da amincin su da kuma ci gaba da ba shi goyon baya.

By ukarofi