Gwamnatin Tarayya ta dakatar da samar da sababbin manyan makarantu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Tarayya ta sanya dokar hana samar da sabbin jami’o’i da polytechnic na tarayya da kwalejin ilimi na tsawon shekaru bakwai, domin rage rashin inganci a harkokin gudanarwa da zuƙe asusun ƙasa.

An yanke haka ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Laraba.

Baya ga haka ne Ministan Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa akwai ƙalubale da dama wajen harkokin gudanarwar makaratun tarayya musamman a rashin wadatattun ababen more rayuwa, maimaita abinda aka jima ana amfani da shi, rashin wadatattun ma’aikata.

Ya ce, a wasu makaratun akan samu inda adadin ma’aikata ya fi yawa akan na ɗalibai musamman a Arewacin Nijeriya, lamarin da a cewarsa ɓarna da dukiyar ƙasa ne.

Ya ƙara da cewa, lallai ne a yi nazari akan makaratun gwamnati da dama game da harkokin gudanarwarsu da sauran al’amuran da suka shafi tafiyar da su bisa tsari don kauce wa samar da ɗalibai marasa nagarta da rage adadin rashin aiki.

Dakta Alausa ya bayyana cewa, dakatarwar da gwamnatin ta yi, zai sa ta samu damar inganta waɗanda ta ke da su a ƙasa da ɗaukar ma’aikatan da suka cancanta da kuma faɗaɗa tsarin ɗibar ɗalibai acikinsu.

By Babaji