Taron TICAD9: Tinubu zai je Japan da Brazil

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A gobe Alhamis, 14 ga Agusta, Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja domin ziyartar ƙasashen Japan da Brazil da nufin ƙarfafa alaƙaƙoƙin Nijeriya da ƙasashen waje kan harkokin zuba jari da ci-gaban ƙirƙira.

Shugaba Tinubu zai kuma bi ta birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a gurguje kana daga bisani ya tafi Yokohama na ƙasar Japan.

A nan ne zai halarci babban taron ƙasa-da-ƙasa akan ci-gaban Afirka karo na tara a birnin Tokyo (TICAD9), wanda za a yi tsakanin ranakun 20 da 22 na Agusta, kamar yadda wata sanarwa daga Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ta bayyana.

A taron, za a mayar da hankali akan hanyoyoyin da za bi wajen bunƙasa harkar tattalin arziƙin Nahiyar Afirka, inganta yanayi na kasuwanci, inganta ayyukan zuba jari ta cibiyoyi masu zaman kansu da kuma harkar ƙirƙira.

Haka kuma, za a tattauna harkokin tsaron ɗan-adam, zamani lafiya, ɗorewa da kwanciyar hankali a sassan Afirka.

Kazalika, Tinubu zai halarci zama tsakanin jagororin ƙasashe da tattauna muhimman al’amura da shugabannin Japan.

By Babaji