Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Majalisar dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano Alhaji Naziru Ya’u na tsawon watanni uku sakamakon rashin Iya tafiyar da mulki da karya dokokin aiki tare da umartar sa ya miƙa aiki ga mataimakin sa.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne yayin zaman da ta gudanar a wannan rana ta Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa an ɗauki matakin ne saboda zargin shugaban ƙaramar hukumar da sayar da tsohuwar kasuwar Rano.

Sannan ana zarginsa da sayar da takin zamani ko karkatar da shi wanda gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rabawa ƙananan hukumomin kano a watan Yulin da ya gabata.

Bayanan da muka samu sun nuna cewa kowace ƙaramar hukuma ta samu tirela uku na takin zamanin mai ɗauke da buhu 600 ko wacce mota.

Kazalika, majalisar ta yi karatu na ɗaya akan ƙudirin dokar ƙwarya ƙwaryar kasafin kuɗi na wannan shekarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata wanda ya kai fiye da naira biliyan 169.

Akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Diso shi ne yayi karatun a yayin zaman majalissar na yau Laraba.

Zaman majalissar wanda shugaban ta Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta ya amince Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Alhaji Sa’id Yahaya a matsayin shugaban hukumar karɓar ƙorafi da hana cin hanci da rashawa ta Jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan rahoton da shugaban kwamitin karɓar ƙorafi na majalissar kuma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Alhaji Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya gabatar.

Ya ce Alhaji Sa’id Yahaya ya cika dukkanin ƙa’idojin da doka ta tanadar kafin naɗa mutum a matsayin shugaban hukumar.

By ukarofi