
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an tsaro a jihar Sakkwato, sun yi nasarar kama Sirajo Ɗan Liman, wanda na’ibin Liman ne a babban masallacin Juma’a na garin Kangiye da ke Gundumar Atakwanyo a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa bisa zargin sa da haɗa hannu da ƴan bindiga a yankin Tanga.
Majiyoyi sun shaida cewa, wasu bayanai na sirri sun nuna cewa na’ibin yana da alaƙa da ƴan bindigar wajen samar musu da babura da wasu kayayyakin aiki da suke amfani da su wajen kai farmaki, yin garkuwa da mutane, sace dabbobi da kutsa wa wasu sassan shiyyar.
A cewar jami’an tsaro, an gano kimanin Naira miliyan 47 a asusun Sirajo, waɗanda ake zargin a ayyukan da ya ke yi da ƴan bindigar ya same su.
Baya ga matsayinsa a masallacin, Sirajo yana da tasiri sosai a harkokin siyasar yankin, domin shi ne shugaban wata jam’iyya a Gundumarsu ta Atakwanyo kuma sakataren ƙungiyar shugabannin jam’iyyu na Gwadabawa.
Haka kuma ya kan jagoranci sallar juma’a a madadin mahaifinsa, wanda shi ne babban limanin da yin wa’azi a wasu lokuta.
