‘Yan dabar Turji sun sake karya alƙawari bayan aikata ta’addanci a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ƴan bindiga daga dabar shahararren jagoransu, Bello Turji, sun kai sabon hari a Ƙauyen Garki da ke jihar Sakkwato, inda suka yi awon-gaba da mutane 16 da halaka ɗaya da kuma ɗebe dabbobi da dama duk da ikirarin ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da wakilan gwamnati.

Rahotanni sun bayyana cewa, harin, wanda ya auku a yammacin ranar Laraba, an yi shi ne ƙarƙashin jagorancin makusancin Turji mai suna Kallamu da ƴan barandarsa.

Wani shaida ya ce, ƴan bindigar sun isa yankin ne a adadi mai yawa inda suka ta yin harbe-harbe, kana daga bisani suka yi garkuwa da mutane da sace wasu dabbobi.

Ƙwararre kan sharhin harkar tsaro, Zagazola Makama ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an ƙaddamar da harin ne a irin salon Turji, inda aka fara da yin harbe-harbe gabannin ɗaukar mutanen.

Al’amarin dai ya haifar da rashin tabbas game da matsayar Turji na kira da a yi sulhu musamman a baya-bayan nan da aka yaɗa na tsakaninsa da malaman addini da wakilan gwamnati.

Sanannen ɗan bindigar ya sha kira da a yi sulhu domin kawo ƙarshen ayyukansu na ta’addanci, saidai ana ganin hakan kamar akwai yaudara a ciki, saboda a duk sadda aka tattauna da shi, daga bisani sai ƴan dabarsa sun kai hari ko garkuwa ko kashe mutane, kamar yadda wata majiya ta tsaro ta shaida.

Rahotannin sirri sun shaida wa manema labarai cewa har yanzu ayyukan ta’addancin Turji na cigaba da gudana a yankunan Isa, Sabon Birni da Goronyo tare da ƴan bindiga da dama da ke kai kawo tsakanin Nijeriya da Nijar.

By Babaji